Ganduje ya gabatar da kasafin kudin jihar Kano, ilimi ya samu babban kaso

Ganduje ya gabatar da kasafin kudin jihar Kano, ilimi ya samu babban kaso

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya mika kasafin kudin shekarar 2020 ga majalisar jihar. Kasafin kudin wanda gwamnan ya sawa suna 'Kasafin cigaba mai dorewa' na dauke da N197,683,353,659 a matsayin jimillar kudin da za a kashe a shekarar 2020 a jihar.

A yayin mika kasafin kudin, gwamnan ya bayyanawa majalisar cewa, N117,710,626,881 a cikin kasafin an waresu ne don manyan aiyuka inda N79,972,726,788 kuma na aiyukan yau da kullum.

Ganduje ya kara da bayyana cewa, ma'aikatar ilimi ce zata samu kaso mafi tsoka na naira biliyan 49.9 wanda ke nuna kashi 25.23 na jimillar kudin. An kuwa yi hakan ne don tabbatar da manyan aiyuka irinsu karatu kyauta kuma na dole daga gwamnatin jihar.

Ma'aikatar ilimin ce a gaba inda take biye da ma'aikatar aiyuka da kayayyakin more rayuwa da ta samu naira biliyan 33.8. Ma'aikatar shugabanci ta samu naira biliyan 33.7 sai lafiya ta samu naira biliyan 30.7. Ma'aikatar ruwa ta samu naira biliyan 15 sai ma'aikatar shari'a ta aka sa wa naira biliyan 7.9.

DUBA WANNAN: Yanzu - Yanzu: Maina ya bayyana a kotu kan keke guragu

Gwamnan yace: "Jimillar kudin shiga na yau da kullum na shekarar 2020 shine N143,900,000,000 wanda ya kunshi N40,000,000,000 a matsayin kudin shiga na cikin gida da kuma N76,000,000,000 shi kuma da asusun tarayya."

"Jimillar kudin shiga na yau da kullum ya ragu da kashi 9 idan aka danganta shi da na shekarar 2019. Shi kuma jimillarkudin shiga na cikin gida ya ragu da kashi 15 idan aka dangantashi da na shekarar 2019," gwamnan ya kara da cewa.

Kakakin majalisar jihar, AbdulAziz gafasa, ya tabbatar da cewa majalisar zata yo iya bakin kokarinta wajen ganin ta aminta da kasafin kudin nan ba da dadewa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel