An kama matar Baghdadi, ta yi bayyana dukkanin sirrin kungiyar ISIS

An kama matar Baghdadi, ta yi bayyana dukkanin sirrin kungiyar ISIS

Jami’an rundunar Sojan kasar Turkiyya sun samu nasarar kama matar tsohon shugaban kungiyar ISIS wanda ya kashe kansa, Abu Bakr Al-Baghdadi, kuma ta bayar da tarin bayanai game da asirin kungiyar da yadda suke tafiyar da ita.

Kamfanin dillancin labaru na AFP ta ruwaito jami’an kasar Turkiyya sun bayyana cewa a shekarar data gabata suka kama matar wanda ta bayyana sunanta a matsayin Rania Mahmoud, amma daga bisani suka gane sunanta na gaskiya Asma Fawzi Muhammad Al-Qubaysi.

KU KARANTA: Aikin jin kai: Aisha Buhari ta tallafa ma mata da matasa 600 a jahar Adamawa

A ranar 2 ga watan Yunin 2018 aka kama Asma, wanda it ace uwargidar Al-Baghdadi, jagoran kungiyar ta’addanci ta ISIS, a yankin Hatay dake daidai iyakar kasar Syria aka kamata tare da wasu mutane 10, daga cikinsu har da diyar Baghdadi, Lelila Jabeer.

Jami’an sun ce sai da suka yi amfani da binciken kimiyya na DNA ta hanyar amfani da jinin Baghdadi da kasar Iraqi ta basu suka tabbatar da cewa lallai Asama Leila iyalan tsohon shugaban ISIS ne.

“Bamu sha wahala ba wajen gano matarsa, daga nan kuma ta bamu bayanan sirri da dama game da ayyukan ISIS, ta wannan hanya mun tabbatar da abubuwa da dama da muka riga muka sani, kuma mun samu karin bayanai da suka taimaka mana wajen kamo wasu mutane a wurare daban daban.” Inji jami’an.

Shi ma shugaban kasar Turkiyya, Recep Erdogan, a karon farko a ranar Laraba ya sanar ma duniya cewa lallai sun kama matar Baghdadi inda yace: “Mun kama matars, yau na fara fadan wannan, amma bamu yi yayatawa ba.”

Haka zalika shugaban yace sun kama kanwar Baghdadi da surukinsa, amma yace basu je suna ta yayatawa kamar yadda Amurka suka dinga yayata batun mutuwar Baghdadi ba.

Baghdadi ya mutu ne a wani samame na musamman da Sojojin Amurka suka kaddamar tare da taimakon Sojojin kurdawa a yankin Arewa maso yammacin lardin Idlib na kasar Syria, inda ya shige wani rami da babu hanyar fita, ganin haka ya tayar da Bom daya kasheshi da yaransa biyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel