Abubuwa 5 da ya sa akace akwai takun saka tsakanin Buhari da Osinbajo

Abubuwa 5 da ya sa akace akwai takun saka tsakanin Buhari da Osinbajo

Yayinda fadar shugaban kasa ta bakin hadiman shugaba Buhari kan harkokin majalisar dokokin tarayya, Babajide Omoworare da Umar EL-Yakub, sune kokarin watsi da rahotannin cewa akwai takun saka tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa, abubuwa sai kara bayyana suke.

Na kusa-kusa shine rahoton cewa shugaba Buhari ya sallami hadiman Osinbajo 35 ya karawa zargin karfi.

Legit.ng ta kawo muku fikafiki biyar da Buhari ya figewa Osinbajo cikin yan kwanaki da suka gabata.

1. Rusa kwamitin tattalin arziki dake karkashin Osinbajo da nada sabuwa wacce ba shi a ciki

A ranar 16 ga Satumba, shugaba Buhari ya rusa kwamitin farfado da tattalin arziki da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, ke jagoranta kuma ya nada sabuwar kwamitin masu bashi shawara kan tattalin arzikin karkashin Farfesa Doyin Salami.

2. Sai Osinbajo ya nemi umurnin Buhari kafin ya aikata komai

A ranar 17 ga Satumba, shugaba Buhari ya bada umurnin cewa sai mataimakinsa ya nemi umurnin Buhari kafin wanzar da wani abu kan ma'aikatun da karkashin ofishin mataimakin shugaban kasa.

Haka ya sabawa yadda suka fara gudanar da mulki inda Osinbajo na da daman aiwatar da abubuwa ba tare da sanar da Buhari ba.

DUBA NAN: Kwastam ta haramta sayar da fetur ga gidajen mai dake da kusancin 20km da iyakokin Najeriya

3. Dauke shirye-shiryen jin dadin al'umma daga karkashinsa zuwa sabuwar ma'aikata

A ranar 1 ga Oktoba, Buhari ya dauke shirin jin dadin al'umma na N-Power, Trader Moni, Market Moni, ciyar da yan makaranta da sauransu daga ofishin mataimakin shugaban kasa zuwa sabuwar ma'aikatar tallafi, jin dadin al'umma da manajin annoba karkashin Hajiya Sadia Umar Farouq.

4. Rattaba hannun Buhari kan dokar harajin mai a Ingila

Sabanin yadda Buhari ya ke yi a baya idan ya tafi Landan na mika ragamar mulki ga Osinbajo, wannan karon Buhari yana mulkan Najeriya daga Ingila. Abin ya kai sai dai Abba Kyari ya kai masa dokar karin kudn harajin hakar mai a ruwa Ingile ya rattaba hannu.

5. Sallamar hadiman Osinbajo 35

A ranar Laraba, rahotannin sun fara bayyana cewa shugaban kasa ya sallami hadiman Osinbajo 35 ba tare da wani laifi da suka aikata ba. Legit.ng ta tabbatar da hakan daga bakin hadimin Buhari kan NSIP, Ismail Ahmad.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel