An haramta rungumar juna tsakanin Malaman jami’a da dalibansu a UNIPORT
Jami’ar gwamnatin tarayya dake garin Fatakwal na jahar Ribas ta kaddamar da sabuwar dokar yaki da cin zarafin dalibai mata, inda tace daga yau ta haramta duk wata alaka data shafi rungumar juna tsakanin Malamai da dalibai Mata.
Shugaban jami’ar, Farfesa Ndowa E.S ne ya bayyana haka a wani taron kaddamar da sabuwar dokar da ya gudana a dakin taro na Ebitime Banigo Hall, inda yace sun samar da wannan doka ne domin tabbatar da kare malamai da dalibai daga cin zarafi.
KU KARANTA: Kyawun alkawari cikawa: Gbajabiamila ya dauki nauyin jaririya mara lafiya, ya saya mata gida a Katsina
Farfesan yace kundin sabuwar ta dokar ta yi bayani dalla dalla game da irin alakar data halatta tsakanin malamai da dalibai a cikin jami’ar, sa’annan ya dauki alwashin hukunta duk wani malami da aka kama da laifin, amma fa yace za su tabbata sun kare mutuncin duk malamin da aka yi ma kazafi.
Farfesa Ndowa yace cigaba da cewa: “Duk wanda aka zargeshi da cin zarafin wata daliba, toh ya shirya kare kansa, haka ita ma duk dalibar da ake zargi da kazafi ta tabbata ta shirya kare kanta domin kuwa dokar babu sani babu sabo.
“Ga duk Malamin daya manta bai fada ma telansa ya sanya masa mazagi a gaban wandonsa ba, shi ma ya yi kuka da kansa, kamar yadda duk dalibar da aka kama tana neman malaminta domin samun maki za ta yi kuka da kanta.” Inji ta.
A wani labari kuma, Shugaban hukumar man fetir ta Najeriya, NNPC, Malam Mele Kyari ya bayyana cewa hukumar NNPC ta kammala kashi na farko na aikin gyarar matatar man fetir dake garin Fatakwal, jahar Ribas.
Kyari ya bayyana haka ne a ranar Talata a yayin wani taron babban zaure a babban birnin tarayya Abuja inda yake zayyana irin nasarorin daya samu tun bayan hawansa mukamin shugabancin NNPC.
Kyari ya bayyana wasu daga cikin nasarorin daya samu sun hada da: kammala kashi na farko na gyarar matatar main a Fatakwal, tsimin kimanin dala biliyan 3 a sashin shari’a na hukumar, hako mai tafkin Kolmani a jahar Bauchi da kuma tara fiye da litan mai biliyan 2.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng