Ana ba Maina beli guduwa zai yi daga Najeriya - EFCC ta laburtawa kotu

Ana ba Maina beli guduwa zai yi daga Najeriya - EFCC ta laburtawa kotu

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta bayyana cewa AbdulRashind Maina ba mutumin kirki bane kuma bai ganin girman dokar Najeriya.

Hukumar ta ce idan har aka bashi beli, tabbas guduwa zai yi daga Najeriya.

Hukumar ta ce Maina ya yi rub da ciki da Bilyan 3 na yan fansho a fili ba tare da wani boye-boye ba.

EFCC ta ce maina na da takardar zaman dan kasar Amurka kuma mazaunin kasar Dubai ne. Duk da cewa fasfot dinshi tayi esfiya, yana fita daga Najeriya ta kasar Nijar ta bodar Sokoto da Katsina.

EFCC ta bayyana hakan a kan karar da ta shigarwa kotu kan Maina dake shirin bukatar beli a babban kotun tarayya dake Abuja.

Ta bukaci Alkalin kada ya baiwa AbdulRashid Maina beli saboda sai da aka sha bakar wahala kafin damkeshi bayan shekaru 7 ana nemansa ruwa a jallo.

Ko da bai gudu ba, yana da makudan kudi a hannunsa kuma zai gurbata shaidun da ake son amfani da su, saboda wasu cikinsu yan'uwasa ne.

DUBA NAN Duk Mai Rigima Da Ganduje Ya Na Batawa Kan Sa Lokaci Ne Kawai - Ministan Tsaro, Magashi

A jiya an samu cikas wajen gurfanar tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho, AbdulRashid Maina, gaban alkalin babban kotun tarayya dake Abuja, Alkali Okon Abang, a yau Talata sakamakon rashin lafiya.

Hukumar EFCC ta kai karar Maina kotun ne kan zargin almundahana, babakere da yaudara na kudin fanshon jama'a kimanin Bilyan dari.

Yayinda kotu ta dawo zama yau Talata, jami'an hukumar gidajen yarin da sauya hali sun gabatarwa Alkalin kotun da wani takardar likitan gidan yarin mai suna, Idowu Ajayi, cewa Maina ya kamu da rashin lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel