Dan takarar gwamnan jam'iyyar ADC da 'yan majalisa 3 za su koma APC

Dan takarar gwamnan jam'iyyar ADC da 'yan majalisa 3 za su koma APC

- Dan takarar gwamna na jam'iyyar ADC, Gboyega Nasiru Isiaka ya ce zai fice daga jam'iyyar ya koma jam'iyyar APC

- Gboyega Nasiru Isiaka ya bayyana hakan ne yayin zantawar da ya yi da manema labarai bayan ganawar sirri da ya yi da gwamnan jihar, Dapo Abiodun a daren ranar Litinin

- Gboyega Nasiru Isiaka ya kuma ce akwai wasu 'yan majalisar dokokin jihar da shugabanin na ADC da za su koma APC tare da shi

Dan takarar gwamnan na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a zaben gwamna a jihar Ogun na ranar 9 ga watan Maris, Prince Gboyega Nasiru Isiaka ya yi nuni ga cewa zai jogoranci wasu 'yan majalisun dokokin jihar uku da wasu shugabannin jam'iyyar don sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar.

DUBA WANNAN: Atiku: Abinda PDP za ta yi bayan ta sha mugun kaye a kotun koli - Chidoka

Daily Trust ta ruwaito cewa Isiaka wanda ya yi takarar gwamna har sau uku a jihar ya yi wannan furucin ne a daren ranar Litinin bayan ya yi ganawar sirri tare da wasu shugabanin jam'iyyar da kuma Gwamna Dapo Abiodun a ofishin gwamnan da ke Abeokuta.

A yayin da ya ke zantawa da manema labarai bayan taron, Isiaka ya ce akwai yiwuwar shi da wasu masu masa biyaya za su sanar da ficewarsu daga jam'iyyar ta ADC cikin 'yan kwanakin nan.

Da aka masa tambaya kan ainihin ranar da za su fice daga jam'iyyar, Isiaka ya ce za a sanar da al'umma matakin da za su dauka nan ba da dadewa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel