Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun budewa motoci wuta a Zuba, Abuja

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun budewa motoci wuta a Zuba, Abuja

Labarin da muka samu da daren nan na nuna cewa wasu yan bindiga sun budewa motocin haya wuta a kusa da dutsen Zuma, hanyar Kaduna-Abuja a daren Talata. Daily Trust ta ruwaito.

Wani wanda ya tsallake rijiya da baya ya bayyana cewa wannan abu ya faru ne misalin karfe 9 na dare da ya shiga mota daga Zuba.

Ya ce harbe-harben ya tilasta jama'a fita daga cikin motocinsu, kowa ya tsere inda kafarsa ta lula.

Wani dan kasuwa mai suna, Hassan Ibrahim, ya bayyana cewa daruruwan fasinjoji sun tsere cikin unguwar Zuma Estate da aka mayar barikin yan sanda yanzu.

Ya ce daga bayan wasu jami'an tsaro sun garzaya wajen da yan bindigan suka bude wuta.

Za ku tuna cewa a watan Oktoba irin wannan abu ya faru a wajen kuma an yi garkuwa da mutane 20.

Sai da aka biya kudin fansa aka sake su.

Har yanzu hukumar yansanda batayi tsokaci kan harin ba kuma duk yunkurin samun jawabi daga bakin kakakin hukumar ya gagara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel