Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game Omotunde-Alade, sabuwar hadimar Buhari

Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game Omotunde-Alade, sabuwar hadimar Buhari

A yau Talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Sarah Omotunde-Alade, a matsayin mai bayar da shawara ta musamman a fannin kudi da tattalin arziki.

Ofishin na nan ne a ma'aikatar kudi, kasafi da tsari na kasa.

Ga wasu abubuwa da yakamata a sani game da Omotunde-Alade:

1. Dakta Sarah Alade ta fara aiki da babban bankin Najeriya ne a shekarar 1993 a matsayin mataimakiyar daraktan bangaren bincike.

2. Ta yi aiki a matsayin shugabar ofishin kudi ta gwamnatin jihohi daga shekarar 1993 zuwa 1996, shugabar ofishin kudi na gwamnatin tarayya daga 1996 zuwa 2000 kuma tayi aiki a sashin kiyasi na haraji daga shekarar 2000 zuwa 2004.

3. An nada Alade a matsayin daraktan aiyukan bankuna ta babban bankin Najeriya a watan Mayu na 2004.

4. Tayi aiki a matsayin shugabar daraktoci, ta tsarin banki da banki kuma tayi sakatariyar kwamitin tsarin biyan kudi na kasa.

5. An zabeta a matsayin mukaddashin gwamnan babban bankin Najeriya a ranar 20 ga watan Fabrairu, 2014 har zuwa lokacin da Godwin Emefiele ya hau kujerar.

6. Dr. Sarah Alade tayi murabus daga babban bankin Najeriya a matsayin mataimakiyar gwamnan bankin bayan shekaru 24 da tayi tana aiki a babban bankin a ranar 22 ga watan Maris, 2017.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel