Yadda masu garkuwa da mutane suka kashe wani bawan Allah bayan karbar kudin fansa

Yadda masu garkuwa da mutane suka kashe wani bawan Allah bayan karbar kudin fansa

Masu garkuda da mutane don karbar kudin fansa sun kashe wani bawan Allah mai suna Sanusi Iro Dabai bayan sun sace shi tare da abokinsa a Jos ta jihar Filato a ranar Litinin da ta gabata duk da cewa iyalan magidanta su biya naira a matsayin kudin fansa.

Mohammed Isa, mai taimakawa shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan na musamman kan kafafen watsa labarai ne ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook kamar yadda Linda Ikeji Blog ya ruwaito.

DUBA WANNAN: Okorocha ya bayyana abinda zai faru da APC bayan 2023

Ya ce an sace Sanusi Iro Dabai ne da abokinsa a kusa da Marabar Jos a ranar Litinin da ta gabata. An kuma gano gawarwakinsu a cikin wani daji bayan an biya masu garkuwa da mutanen miliyoyin naira. Ya yi addu'an Allah ya jikansu da rahama kana ya tona asirin wadanda suka aikata wannan mummunan aikin.

Ga abinda ya rubuta: "Innalilahi wa'inna ilaihi raji'un. An sace Sanusi Iro Dabai tare da abokinsa kusa da Marabar Jos a ranar Litinin da ta gabata. An gano gawarsu da ta fara rubewa a yammacin yau bayan an biya miliyoyin kudi ga masu garkuwa da mutanen. Allah ya jikansu, ya gafarta musu. Su kuma Allah ya tona asirinsu"

Hoton wani bawan Allah da masu garkua da mutane suka kashe bayan sun karbi kudin fansa
Hoton wani bawan Allah da masu garkua da mutane suka kashe bayan sun karbi kudin fansa
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel