Atiku: Abinda PDP za ta yi bayan ta sha mugun kaye a kotun koli - Chidoka

Atiku: Abinda PDP za ta yi bayan ta sha mugun kaye a kotun koli - Chidoka

Jigo a jam'iyyar PDP, Osita Chidoka, ya tabbatar da cewa, jam'iyyar ta rungumi hukuncin kotun koli da ta tabbatar wa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kujerar shugabancin kasa duk da hakan bai yi musu dadi ba.

Duk da jam'iyyar bata gano dalilin hukuncin kotun kolin ba amma ta yanke shawarar cigaba da gina damokaradiyyar cikin gida, a jawabin da ya yi yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Juma'a, kamar yadda The Nation Online ta ruwaito.

Atiku da Peter Obi duk masu biyayya ne ga damokaradiyya. Hakazalika jam'iyyar PDP. Hukuncin ya yi banbarakwai kuma mun kasa gano dalilin hukuncin amma mun rungumi hukuncin. Abin duba yanzu shine yadda zamu gina Najeriya, in ji jigon.

DUBA WANNAN: Okorocha ya bayyana abinda zai faru da APC bayan 2023

Ya kara da cewa, "PDP na hangen gaba ne. Shugaban jam'iyyar na kasa, Uche Secondus zai kaddamar da shirye-shirye masu yawa tare da kawo tsarin gyara da gina jam'iyyar tun daga matakin kasa har zuwa gundumomi.

"Hakan kuwa zai kawo gyara ga damokaradiyyar cikin gida. Zamu samu tabbacin cewa jam'iyyarmu tayi karfin da zata iya fuskantar duk wani zabe nan gaba."

A halin yanzu jam'iyyar PDP ta fara fahimtar amfanin hadin kan cikin gida wanda hakan ne zai zamo jigon nasararta a 2023.

A yayin da alkalan kotun kolin da suka samu jagorancin shugaban alkalai, Tanko Muhammad basu sanar da dalilin yanke hukuncin ba, ya ce, PDP ta bayar da nagartattun shaidu a kararta amma sam kotun bata duba hakan ba, tayi watsi da karar.

"Ko masu lura da zabe daga kasashen ketare sun tabbatar da cewa ba a yi zaben gaskiya ba. A tunanina, kotu yakamata ta ganar da 'yan siyasa cewa ba ta karfi ake cin zabe ba, tunda mulkin damokaradiyya akeyi," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel