'Yan kasuwa sunyi zanga-zanga kan kwace buhunan kwakwa 1,450 da Kwastam ta yi

'Yan kasuwa sunyi zanga-zanga kan kwace buhunan kwakwa 1,450 da Kwastam ta yi

A ranar Litinin ne 'yan kasuwar kwakwa da ke Badagry suka yi zanga-zanga aka kwace buhuna 1,450 na kwakwar gida Najeriya da hukumar kwastam ta kasa tayi a jihar Legas, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

'Yan kasuwar, karkashin shugabancin kungiyar masu sayar da kwakwar sun yi zanga-zanga ne har zuwa fadar sarkin Badagry da kuma sakatariyar karamar hukumar da ke Ajara.

Babban sakataren kungiyar kuma mai magana da yawun kungiyar, Tinde Hunpatin, ya ce anyi zanga-zangar ne don nuna rashin jin dadi akan kwace kwakwar da aka yi da kuma hantarar 'yan kasuwar da jami'an kwastam din ke yi.

DUBA WANNAN: Okorocha ya bayyana abinda zai faru da APC bayan 2023

Ya ce, "A yammacin ranar 27 ga watan Oktoba, motocin kaya biyu tare da wata motar hawa daya da ke dauke da kwakwar gida suna hanyar zuwa wajen sarrafa kwakwar don masu siye amma kwastam suka taresu tare da kwace kayan,"

"Motocin na ofishin yanki na daya na hukumar kwastam din. Daga zuwansu Ikeja, har an fitar da lokacin gwanjansu ba tare da an dubasu ba."

A fadar sarkin, shugaban kungiyar ya roki mai martaba Aholu Meno Toyi da ya cece 'yan kasuwar a kan hantararsu da jami'an keyi tare da taimakawa wajen sa baki don jami'an su sakar musu kayansu.

"Kwakwarmu ba daga Ghana take ba; jami'an tsaron su duba da kyau," in ji shi.

Akran yayi wa fusatattun 'yan kasuwar alkawarin zai shiga lamarin tare da tabbatar musu da cewa, kasuwar ta kwakwa dake kasar shi ba zata mutu ba.

Mai magana da yawun hukumar kwastam din Najeriya, Jerry Attah, bai dauki kiran da aka dinga mishi ba kuma bai maida martani akan sakon karta kwanan da aka tura mishi ba akan zargin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel