Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta fitittiki Ado Doguwa

Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta fitittiki Ado Doguwa

Kotun daukaka kara dake zaune a jihar Kaduna a ranar Litinin ta fitittiki dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltan mazabar Tudun Wada/Doguwa kuma shugaban masu rinjaye a majalisa, Alhassan Ado Doguwa.

Ado Doguwa ne mutum mafi girman kujera na uku a majalisa bayan Kakakin majalisa da mataimakinsa.

Kotun ta yi watsi da zaben kananan hukumomi biyu da Ado Doguwa ke wakilta kan zargin magudin da aka tafka a zaben Febrairun 2019.

Alkalan kotun karkashin jagorancin Alkali Oludotun Adefope-Okojie,sun yi ittifakin cewa ba zai yiwu a amince da sakamakon zaben ba saboda babu sunayen wasu yan takara a takardan sakamakon da INEC ta sanar.

Kotun ta ce hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta ta tafka babban kuskuren rubuta sakamakon jam'iyyu biyu kadai cikin 53 da sukayi takara.

Ku saurari cikakken rahoton...

DUBA WANNAN N140,000 na siya yaran 2 - Mijin matar aka damke a tasha tana kokarin guduwa Onitsha da yara Hausawa

Gabanin wannan A ranar Juma'a ne kotun daukaka kara ta soke zaben dan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru/Bebeji a majalisar dattawa kuma ta bada umarnin yin sabon zabe, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Kotun daukaka karar ta soke dukkan zaben da aka yi a kananan hukumomin biyu sakamakon ganowa da tayi cewa sakamakon zaben na karshe da aka cike Fom EC(8)E lalatacce ne.

Mai shari'a Adedotun Adfoke-Okoji yayin yanke hukuncin ya ce, tunda an lalata sakamakon, babu yadda za a yi a gano asalinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel