Sanar da sakamako bayan kwana 5 da kammala zabe: PDP ta garzaya kotu a kan zaben jihar Kebbi
Jam'iyyar PDP a jihar Kebbi ta yi watsi da sakamakon zaben kananan hukumomin jihar da hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Kebbi (KSIEC) ta sanar.
An gudanar da zaben kananan hukumomin jihar Kebbi ne a ranar 26 ga watan Oktoba amma KSIEC bata sanar da sakamako ba sai bayan kwanaki biyar.
Yayin ganawarsa da manema labarai a Birnin Kebbi, shugaban jam'iyyar PDP a jihar Kebbi, Mallam Haruna Saidu, ya ce sakamakon zaben bai yi daidai da zabin masu kada kuri'a ba a zaben da aka gudanar.
"Jam'iyyar PDP ta yi Alla-wadai tare da yin watsi da sakamakon balagurbin zaben da hukumar zabe ta gudanar a jihar Kebbi.
"Sakamakon zaben da KSIEC ta gabatar ba daidai bane, a saboda haka, jam'iyyar PDP da mutanen jihar Kebbi ba zasu karbi wannan sakamakon zaben ba," a cewarsa.
A cewar Mallam Saidu, jam'iyyar PDP ta samu nasarar lashe zabe a kananan hukumomin Argungu, Zuru, Augie, Aliero, Jega, Sakaba da Gwandu. Kazalika, ya bayyana cewa jam'iyyarsu, PDP, ta samu nasarar lashe kujerun Kansiloli fiye da 40, sabanin guda shidda da KSIEC ta sanar ta lashe.
DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane da 'yan fashi 72 a Bauchi
Ya bayyana cewa sai da KSIEC ta dauki tsawon kwanaki biyar kafin ta gabatar da sakamakon zaben da ta gama yiwa kwaskwarima domin yiwa jam'iyyar PDP fashin nasarar da ta samu a zaben da aka gudanar mai cike da rigingimu da magudi.
"Mun kammala dukkan shirye-shiryen garzaya wa kotun sauraron korafin zabe domin neman hakkinmu, kuma ba zamu hakura sai mun ga inda shari'a ta kare.
"A saboda haka nake kira ga mambobin jam'iyya da masu zabe da sauran masoya jam'iyyar PDP da su kwantar da hankalinsu domin ba zamu hakura ba, sai mun bi kadin hakkin mu," a cewar shugaban jam'iyyar.
Hukumar KSIEC ta bayyana cewa jam'iyyar APC ce ta samu nasarar lashe dukkan kujerun ciyamomin kananan hukumomin jihar Kebbi guda 21 tare da sauran kujerun Kansiloli, wadanda PDP ta samu nasarar lashe guda shidda.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng