Abdulmumin Kofa ya yi martani kan hukuncin kotun daukaka kara na soke zabensa

Abdulmumin Kofa ya yi martani kan hukuncin kotun daukaka kara na soke zabensa

Dan majalisar wakilai daga Kano mai wakiltar Kiru/Bebeji a Majalisar Dokoki na Tarayya, Abdulmumin Jibrin, ya mayar martani a kan hukuncin kotun koli da ta soke zabensa.

Jibrin ya ce, hukuncin abin al'ajabi ne kuma bai bi dokar shari'a ba.

A ranar Juma'a ne kotun daukaka karar ta kwace kujerar dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji a tarayya daga jihar Kano kuma ta bayar da umarnin yin sabon zabe.

Kotun daukaka karar ta soke duk zaben da aka yi a kananan hukumomin biyu ne sakamakon Form EC (8) E da aka cike da sakamakon da ba shi ne ba.

DUBA WANNAN: Kujerar Sanata: PDP ta sake lallasa tsohon gwamnan APC a kotun daukaka kara

A yayin mayar da martani kan lamarin, Jibrin ya ce, "Kamar yadda kuka sani, hukuncin mutanen Kiru da Bebeji shine sabunta yardar da suka dani don wakiltarsu a majalisar tarayya. Amma wasu sun kai kararsu kotu inda suke kalubalantar hakan,"

"A karar, an bukaci kotun da ta soke sakamakon akwati 13 ne a zaben 23 ga watan Fabrairu. A akwatuna 13, shaida daya ne wanda masu karar basu gabatar ba amma ya gabatar da kanshi a matsayin dan jam'iyyar APC da PDP, ya bayar da shaida a kan akwatunan 13,"

"Shaidar bai da gamsassun bayanai da zai ce ya halarci duk wajen akwatuna 13. Munyi nuni da hakan ga masu shari'a da kuma kotun sauraron kararrakin zabe wacce ta yi watsi da karar da farko,"

"Masu karar sun daukaka kara kuma hukuncin kotun ne ya kai ga kwace kujerar. Wannan abun al'ajabi ne tunda bukatar masu karar shine a canza zabe a akwatunan amma sai gashi an soke zaben gabadaya,"

"A matsayina na musulmi nagari, dole ne in yi imani da Allah. Na yarda cewa duk abinda zai faru karkashin ikonsa ne. Amma babu shakka ban aminta da hukuncin kotun daukaka kara ba. A matsayina na wanda aka raina a dimokradiyya, ina kira ga magoya bayana da mu koma don sake zaben. Har yanzu ina da tabbacin ni ne zabin mutanen Kiru da Bebeji. Tunda suka zabeni da farko, ba shakka zasu kara zabena."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel