Gwamna Zulum ya nada kwamiti na musamman kan gobarar kasuwar Jagwol (Kalli hotunan annobar)

Gwamna Zulum ya nada kwamiti na musamman kan gobarar kasuwar Jagwol (Kalli hotunan annobar)

A daren Alhamis, 31 ga Agusta, 2019, gobara ta lashe kasuwar sayar da wayoyi da aka fi sani da Kasuwa Jagwol dake Maiduguri, birnin jihar Borno.

Wannan abun ya faru yayinda gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ke Saudiyya tare da shugaba Muhammadu Buhari domin halartan taron sanya hannun jari da gabatar da ibadar Umrah.

Daga Saudiyya, Gwamnan Babagana Umara Zulum, ya umurci shugaban ma'aikatansa, Babagana Wakil, da wasu kwamishanoni biyar su kai ziyara kasuwar kuma su duba irin asarar da akayi domin sanin irin taimakon da gwamnatin za tayi.

Yace: "Na umurci shugaban ma'aikatan gidan gwamnatina, Dakta Babagana Wakil, ya sammaci kwamishanonin da ma'aikatunsu ya shafi kasuwanci, harkokin gida, yaye talauci da samar da aiki suyi gaggawan duba gobaran daren Alhamis a kasuwar GSM."

"Kuma su bani rahoto ranar Litinin."

"Allah ya kiyaye gaba. Kuma insha Allahu za mu taimakawa wadanda abin ya shafa."

Kalli hotunan:

Gwamna Zulum ya nada kwamiti na musamman kan gobarar kasuwar Jagwol (Kalli hotunan annobar)
Hoto mallakan Channels TV
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel