Sarkin Gombe ya kaiwa Nasir El-Rufa'i ziyara Kaduna (Hotuna)

Sarkin Gombe ya kaiwa Nasir El-Rufa'i ziyara Kaduna (Hotuna)

Gwamnan jihar Kaduna , Nasir Ahmed El-Rufai, tare da mataimakiyar, Dakta Hadiza, sun karbi bakuncin mai martaba sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, a gidan gwamnatin jihar Sir Kashim Ibrahim House.

Sarkin ya kawo ziyara jihar ne a ranar Juma'a, 1 ga Nuwamba 2019.

Bayan tattaunawa da sukayi, sun garzaya babban Masallacin Sultan Bello dake unguwar Sarkin jihar Kaduna domin gabatar da Sallar Juma'a.

Wannan ya biyo bayan zuwa mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu a jiya Alhamis yayinda gwamna El-Rufai ne ya gayyaceshi domin ya gabatar da jawabi ga wasu matasa 18 dake cikin gajiyar tsarin horaswa a sha’anin mulki da gwamnan ya kirkiro mai taken Sir Kashim Ibrahim Fellows.

KU KARANTA: An damke wata mata ta sace dan jaririn wata hudu

A wani labarin kuma, wata kungiyar magoya bayan gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai mai suna Nasirriya sun bude wani ofishin yakin neman zaben El-Rufai a matsayin shugaban kasar Najeriya a shekarar 2023 a garin Jos na jahar Filato.

Shugaban Nasiriyya, Hajiya Nafisatu Omar ta bayyana cewa El-Rufai ya cancanci zama shugaban kasar Najeriya saboda mutum ne da baya nuna bambamcin addini ko kabilanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel