An damke wata mata ta sace dan jaririn wata hudu

An damke wata mata ta sace dan jaririn wata hudu

Hukumar yan sandan jihar Ogun ta damke wata mata mai suna Falilat Olatunji da laifin satar jariri dan wata hudu a jihar.

A cewar kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, an damke matar ne bayan wani makwabcinta ya kai kararta ofishin hukumar dake Sabo Ilupeju.

Kakakin yace: "Wata mata mai suna Taiwo Bello na wanki a bayan gidanta a unguwar Iyana kajola mile 2 Abeokuta, ta bar dan jaririnya Ibrahim Bello yana kwance cikin dakinta. Kafin ta daow, sai ta ga an yi awon gaba da jaririn."

"Makwabcin ya kara da cewa hankalin matar ya tashi kuma jama'a suka taru a kofar gidan."

"Bayan samun labarin, DPO na ofishin Sabo Ilupeju, CSP Alhassan AbdulAzeez, ya tura jami'ansa su kammala bincike kan lamarin."

"Kokarinsu ya haifar da 'da mai ido inda aka ganta a unguwar Ilewo Orile da jaririn kuma aka damketa."

"Yayin bincike, matar ya laburta cewa ta sace yaron ne kawai don nunawa mijinta da ta yiwa karar cewa ta haihu."

"Binciken ya bayyana cewa matar ta zauna gida daya da iyayen jaririn da ta sace kuma ta halarci taron sunan jaririn."

An mayar da yaron ga iyayensa a yanzu.

DUBA: Buhari ya dira Makkah domin gabatar da Ibadar Umrah, ya samu kyakkyawan tarba

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel