Buhari ya dira Makkah domin gabatar da Ibadar Umrah, ya samu kyakkyawan tarba (Bidiyo)

Buhari ya dira Makkah domin gabatar da Ibadar Umrah, ya samu kyakkyawan tarba (Bidiyo)

Da yammacin Alhamis, Shugaba Muhammadu Buhari ya isa birnin Makkah, domin gabatar da ibadar Umrah bayan kammala halartan taron sanya hannu jari na tsawon kwana uku a birnin Riyadh.

Shugaba Buhari ya dira filin jirgin saman Sarki AbdulAziz ne misalin karfe 7:05 na Magariba.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta bada rahoton cewa shugaba Buhari ya samu kyayyakwar tarba daga wajen mataimakin gwamnan garin Makkah, Bader bin Sultan bin AbdulAziz da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar a filin jirgin saman Sarki AbdulAziz.

Tuni shugaba Buhari da wadanda suka rakashi sun sanya izari da rida'i.

Daga cikin wadanda zasu gudanar da Umrah tare da shi sune gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari; gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu da sauransu.

Kalli bidiyon:

Bayan kammala Umrah a Makkah, shugaba Buhari zai garzaya kasar Ingila domin hutawa inda zai kwashe makonni biyu a birnin Landan.

Rahotannin sun nuna cewa Buhari jinya zai tafi yi Landan kamar yadda ya sha faruwa a shekarun baya idan yayi irin wannan tafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel