Akalla mutane 65 sun hallaka yayinda tukunyar gas ya fashe cikin jirgi

Akalla mutane 65 sun hallaka yayinda tukunyar gas ya fashe cikin jirgi

Akalla mutane 65 sun rasa rayukansu yayinda da yawa sun jikkata sakamakon fashewar tukungar gas cikin jirgin kasan mahajjata a kasar Pakistan ranar Alhamis.

Bidiyo yanuna yadda jirgin kasan ke ci bal-bal da mutane a ciki kuma ana jin iwun wadanda wutan ya rutsa da su a garin Punjab.

Wasu fasijojin sun kasance mahajjatan da suke nufin zuwa taron addininsu inda wasu suka fara girki cikin jirgin da tukunyar Gas. Kawai sai tukunyar gas biyu suka fashe, Ali Nawaz, babban jami'in jirgin kasan ya laburta.

Nawaz ya kara da cewa an yarda matafiya su hau jirgi da kayayykin abinci amma ba'a amince suyi girki da tukunyan gas ba.

Jami'an kwana-kwana sun dira wajen domin kashe wutar amma da dama sun rigaya da konewa.

Ministan kiwon lafiya, Yasmin Rashid, ta tabbatar da labarin.

Kalli bidiyon:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel