Ajali ya yi kira: Tsohon gwamnan jahar Legas ya mutu

Ajali ya yi kira: Tsohon gwamnan jahar Legas ya mutu

Rahotanni sun tabbatar da mutuwar tsohon gwamnan jahar Legas na mulkin Soja na farko, Birgediya Mobolaji Olofunso Johnson mai ritaya a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoban shekarar 2019.

Jaridar Blue Print ta ruwaito Johnson ya mutu yana dan shekara 83 a duniya, kamar yadda dansa, Deji ya tabbatar, inda ya tabbatar da cewa a ranar Laraba mahaifinsa ya mutu.

KU KARANTA: Ya kamata Atiku da PDP su rungumi kaddara - Sanata Ahmad Lawan

A shekarar 1936, ranar 9 ga watan Feburairu aka haifi Johnson, sunan mahaifinsa Joshua Motola Johnson yayin da mahaifiyarsa take Gbemisola Johnson.

Johnson ya zama gwamnan mulkin Soja na farko a jahar Legas ne a shekarar 1966 bayan shugaban kasar na Najeriya na mulkin Soja na farko, janar Aguiyi Ironsi ya amshi mulki.

Haka zalika ko bayan kifar da gwamnatin Ironsi, sabon shugaban Najeriya na wancan lokaci, Janar Yakubu Gowon ya sake nadashi gwamnan Legas daga ranar 28 ga watan Mayu na shekarar 1967 zuwa watan Yuli na shekarar 1975.

A shekarar 1975 Johnson ya yi ritaya daga aikin Soja, inda ya fantsama cikin harkokin kasuwanci, a shekarar 1979 ya zama darakta a kamfanin gine gine na Julius Berger, yayin da a shekarar 1996 ya zama shugaban kamfanin, mukamin da ya rike har zuwa 2009.

A wani labarin kuma, ma’aikatar tsaro ta kasar Nijar ta bayyana cewa Sojoji 12 ne suka gamu da ajalinsu yayin da gungun mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suka kai musu farmaki a wani sansanin Sojoji dake yankin Diffa na kasar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel