Kawai ka hada kai da APC - Tinubu ya shawarci Atiku

Kawai ka hada kai da APC - Tinubu ya shawarci Atiku

Babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Sen. Bola Tinubu, a ranar Laraba ya yi kira ga dan takarar PDP, Atiku Abubakar, ya hada karfi da karfe da APC wajen ciyar da kasa gaba.

A jawabin da ya daura shafin ra'ayi da sada zumuntarsa kan hukuncin kotun koli, Tinubu ya yabawa da PDP da Atiku kan kokarin da yayi na zuwa kotu domin sanin sihhancin kayarwan da ya sha a zabe.

Hakazalika Tinubu ya yabawa kotun koli kan irin namijin kokarin da Alkalan sukayi wajen yanke hukunci cikin dan kankanin lokaci.

Yace: "Yanzu kawai Atiku ya yi amfani da kwakwalwarsa da karfinsa da yayi amfani da shi wajen hada kai da APC domin ciyar da kasa gaba."

"A ranar 23 ga Febrairu, mutane sun bayyana ra'ayinsu na demokradiyya ta hanyar sake zaben shugaba Muhammadu Buhari."

KU KARANTA: Buhari ya halarcin taron cigaban nahiyar Afrika a Saudiyya

A nashi tsokacin, Atiku Abubakar ya bayyana bacin ransa da takaici kan hukunicn kotun koli da yadda yadda bangaren shari'a, yan jarida, da hukumar zabe ta INEC ba su da karfi a Najeriya.

Atiku ya ce wannan shari'a ya nuna cewa dukkan abinda PDP ta gina a shekaru 16 da tayi mulki na kawo cigaban demokradiyya, wannan gwamnatin ta rusa su.

A karshe ya mika godiyarsa ga yan Najeriya da suka nuna masa goyon baya da soyayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel