Duk tafiye-tafiyen Buhari bai kai Obasanjo ba, inji Oshiomhole

Duk tafiye-tafiyen Buhari bai kai Obasanjo ba, inji Oshiomhole

- Shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomhole, ya ce ba daidai bane ikirarin da ake yi kan yawan yawon shugaban kasa Muhammadu Buhari

- A cewar shugaban jam'iyyar, tsohon shugaban kasa Obasanjo ya fi Buhari yawon yawace-yawace zuwa kasashen ketare

- Ya kara da bayyana cewa, marigayi Gani Fawehinmi har kokari yayi wajen tattara jimillar kwanakin da Obasanjo ya diba a kasashen ketare saboda tsananin yawonsa a cikin shekaru 8 na mulkinsa

Shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomhole, ya ce ba dai-dai bane ikirarin da mutane suke yi akan yawan yawon shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa kasashen ketare.

Oshiomhole, wanda ya amsa tambayoyin manema labarai a ranar Laraba a Abuja, yace shugaban kasa Muhammad Buhari ba zai taba kamo tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ba a fannin yawo zuwa kasashen ketare.

DUBA WANNAN: Assha: Sarki ya sallami fadawarsa biyu da aka kama suna aikata zina

Ya kara da bada misali da abinda ke cikin littafin marigayi Gani Fawehimi a inda ya lissafa yawan kwanakin da Obasanjo yayi a yawon zuwa kasashen ketare a cikin shekaru 8 da yayi yana mulki.

"Cewa shugaban kasa ya cika yawo kuskure ne. Zan iya tuna tarihi tsaf, babu shugaban kasar da aka yi tun 1999 da ya kai tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yawan yawo. Akwai kididdigar da marigayi Gani Fawehinmi yayi na kwanakin da tsohon shugaban Obasanjo ya share a kasashen ketare."

"Ya yi kokarin kirga jimillar sa'o'in da yake a jirgi tare da dangantasu da wadanda yake yi a Najeriya. Toh ta yaya da wayonku lokacin amma zaku dinga cewa Buhari yana yawo? Hakan ba daidai bane," in ji shugaban APC na kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel