Musulunci: Sultan ya bayar da hutun ranar 1 ga watan Rabiul-Awwal

Musulunci: Sultan ya bayar da hutun ranar 1 ga watan Rabiul-Awwal

- Mai girma sarkin musulmi kuma shugaban Majalisar Koli ta addinin musulunci a Najeriya ya bayyana yau Laraba a matsayin daya ga watan Rabi'ul-Awwal

- Sarkin musulmin ya sanar da hakan ne a takardar da shugaban kwamitin bada shawarwari akan addinin Islama, Farfesa Sambo Wali Junaidu yasa hannu

- Yau ta kasance daya ga watan ne sakamakon neman jinjirin watan da aka dinga yi tun ranar Litinin ba a gansa ba

Sarkin musulmi kuma shugaban majalisar koli ta al'amuran addinin musulunci, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar, ya bayyana yau Laraba, 30 ga watan Oktoba, 2019 a matsayin 1 ga watan Rabi'ul Awwal, shekaru 1441 bayan hijirar fiyayyen halitta, Annnabi Muhammad.

DUBA WANNAN: Assha: Sarki ya sallami fadawarsa biyu da aka kama suna aikata zina

Daily Trust ta ruwaito cewa Sultan Abubakar ya sanar da hakan ne a wata takarda da shugaban kwamitin bada shawara na lamurran addinin musulunci, Farfesa Sambo Wali Junaidu, yasa hannu.

Takardar ta yi bayanin cewa, kwamitin bayar da shawara akan lamurran addinin musulunci tare da hadin guiwar kwamitin neman wata na kasa basu samu wani rahoton ganin watan ba, wanda hakan ne ya tabbatar da yau Laraba ta zamo daya ga sabon watan.

Takardar ta ce, "Mai girma Sarkin musulmi ya aminta da cewa yau Laraba ta zamo 1 ga watan Rabi'ul-Awwal, 1441 bayan hijirar Manzon tsira."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel