Yadda fate fate ya halaka wasu yan biki guda 3, ya jikkata 2 a jahar Bauchi

Yadda fate fate ya halaka wasu yan biki guda 3, ya jikkata 2 a jahar Bauchi

Wani lamari mai ban tausayi ya janyo ma wasu amarya da ango, Hafsat da Babangida tashin a hankali a yayin bikin aurensu, inda abincin yan biki da aka tanada don gudanar da taron ‘ranar kauyawa’ ya halaka wadanda aka tanadeshi don su.

Jaridar Leadership ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a unguwar Yakubu Wanka dake cikin garin Bauchi, a ranar 2 ga watan Oktoba inda wata Keke Napep dake dauke da faten tare da yara yan biki ta kife a kan hanya.

KU KARANTA: Mutumin da ya tsula fitsari a gaban Alkali ya samu belin N50,000

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan hadari ne ya yi sanadiyyar kifewar faten kamar yadda babur din ta kifa, da haka ta zube gaba daya a kan yaran dake mata rakiya su 5 tare da konasu. Yaran dai sun hada da; Ibrahim Muhammad, Maryam Muhammad, Asiya Sulaiman, Nana Khadija Usman da kuma Sadik Musa.

Rahotanni sun bayyana cewa sakamakon tsananin raunin da suka samu ya yi ajalin Ibrahim dan wata 9 a duniya inda ya rasu a washe garin aukuwar hadarin, Asiya yar shekara 6 ta rasu bayan kwana 2, sai Maryam yar shekara 12 ta rasu a ranar 19 ga wata.

Zuwa yanzu dai Nana Khadija Usman yar shekara 10 da dan uwanta Sadik Musa dan shekara 7 suna can suna jinyar munanan raunin da suka samu a wani asibiti.

Da wannan ne iyayen masu wannan biki suka yi alwashi ba zasu sake bari wani dan gidansu ya shirya bikin kauyawa day ba saboda wannan lamari daya faru ya zamto izina a garesu, haka nan ma wani daga cikinsu yace zai yi wuya a sake girka fate a gidan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel