Yanzu-yanzu: Wata 'yar Najeriya ta sake samun babban mukami a Majalisar Dinkin Duniya

Yanzu-yanzu: Wata 'yar Najeriya ta sake samun babban mukami a Majalisar Dinkin Duniya

- An bawa Damilola Ogunbiyi babban mukami a majalisar dinkin duniya (UN)

- An kuma nada Ogunbiyi a matsayin shugaban SEAforALL

- Ogunbiyi ce mace ta farko da ta jagorancin hukumar samar da lantarki ga karkara ta Najeriya

Wata 'yar Najeriya, Damilola Ogunbiyi ta shiga jerin 'yan Najeriya suka samu muhimman mukamai a duniya bayan an ba ta babban mukami a majalisar dinkin duniya wato UN.

Sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres ne ya nada Ogunbiyi a matsayin wakiliya ta musamma kan samar da makamashi ga kowa (SEforALL) da kuma shugaba na sashin makamashi.

An sanar da nadin Ogunbiyi ne a ranar Talata cikin wani sako da aka wallafa a shafin intanet na UN.

DUBA WANNAN: APC ta fallasa wani makirci da Atiku da PDP ke shiryawa alkalan kotun koli

Legit.ng ta kuma gano cewa an kuma nada Ogunbiyi a matsayin shugaban SEforALL.

SEforALL kungiya ce ta kasa da kasa da ke da hedkwatan ta a Vienna a Austria. An kafa kungiyar ne don taimakawa duniya cimma muradun karnin guda ta 7 (SDG7) da kuma Paris Agreement.

SDG7 ya mayar da hankali ne kan samar da lantarki da makamashi mai tsafa da araha ga dukkan al'ummar duniya kafin 2030.

Ogunbiyi ce mace ta farko da aka taba nadawa a matsayin shugaban Hukumar Samar da Lantarki a Karkara ta Najeriya (REA).

Kafin nadin ta a matsayin shuganan REA, Ogunbiyi ce babban manaja a Hukumar Samar da Wutan Lantarki na jihar Legas kuma ita ce mace ta farko da ta taba rike mukamin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel