Yanzu-yanzu: Adam A Zango ya mikawa sarkin Zazzau fom 101 na yaran da ya biyawa kudin makaranta (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Adam A Zango ya mikawa sarkin Zazzau fom 101 na yaran da ya biyawa kudin makaranta (Hotuna)

A ranar Talata, 29 ga Oktoba shahrarren mawaki kuma dan wasan kwaikwayo, Adam A Zango, ya kai ziyara ta musamman fadar mai martaba sarkin Zazzau, Alhaji Dakta Shehu Idris.

Adam A Zango tare da mukarrabansa sun hallara gaban mai martaba ne domin mika masa takardan neman shiga makaranta wato Fom na dalibai 101 da ya biyawa kudin makaranta.

Adam Zango ya raba Fom din gida biyar: Masarauta, yan darika, yan Izalah, jam'iyyar APC, da PDP.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Adam A. Zango, ya dauki nauyin karatun yara 101 a makarantar 'Professor Ango Abdullahi International School' da ke garin Zaria.

Kamfanin shirya fina-finai na Adam Zango, watau 'Price Zango Production Nigeria Limited', ya biya makarantar miliyan N46.75 a mastayin kudin daukar nauyin daliban na tsawon shekaru uku.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumuta (Instagram), Zango ya bayyana cewa, "ina jin dadin samun damar taimakon masu karamin karfi. Yana daga cikin burin rayuwata na taimaki jama'a, musamman kananan yara, ina jin dadin yin hakan, saboda yana saka ni farinciki.

Shugaban makarantar, Malam Hamza Jibril, ya tabbatar wa da manema labarai cewa jarumin ya biya kudin daukar nauyin daliban.

Kalli hotunan:

Yanzu-yanzu: Adam A Zango ya mikawa sarkin Zazzau fom 101 na yaran da ya biyawa kudin makaranta (Hotuna)
Zango
Asali: Facebook

Yanzu-yanzu: Adam A Zango ya mikawa sarkin Zazzau fom 101 na yaran da ya biyawa kudin makaranta (Hotuna)
Adam A Zango ya mikawa sarkin Zazzau
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel