Yarinyar da ta shekara ana nemanta ruwa a jallo, a karshe mahaifiyarta ta ganta a cikin fim din batsa

Yarinyar da ta shekara ana nemanta ruwa a jallo, a karshe mahaifiyarta ta ganta a cikin fim din batsa

- Wata yarinya da aka kwashe kusan shekara daya ana nemanta ba a ganta ba, a karshe an ganta ta fito a wani fim din batsa

- Yarinyar dai an hada ta da iyayenta yanzu, kuma an kama mutumin da yake da hannu wajen batan nata

- Yarinyar ta bayyana cewa mutumin yayi mata ciki kuma ya dauke ta ya kaita asibiti domin a zubar da wannan ciki

Wani fim din batsa na wata yarinya da ta shekara da bata yayi sanadiyyar da ya sanya ta hadu da iyayenta, inda kuma aka kama wani mutumi dan shekara 30 mai suna Christopher Johnson a yankin Fort Lauderdale dake kudancin birnin Florida.

Yarinyar da aka tilasta ta zubar da ciki bayan ta samu juna biyu lokacin da ta fara wannan sana'a, a yanzu haka dai tayi fina-finan batsa guda 58 inda aka nuno ta a shafukan haska fina-finan batsa irin su Periscope, Modelhub, Snapchat, Pornhub da dai sauran su.

'Yan sanda sun samu nasarar gano yarinyar bayan sun gano wani saurayi da ya fito a daya daga cikin bidiyon da yarinyar ta yi. Yarinyar wacce aka bayyana cewa ta bata an samu nasarar ganinta a wani shagon sayar da kaya duk kuwa da cewa tayi kokarin rufe fuskarta kafin daga nan suka gudu a wata mota kirar Dodge Challenger.

Motar dai an gano cewa ta Christopher Johnson ce kuma yarinyar ta bayyana cewa da yawa daga cikin bidiyon da tayi na batsan a gidan shi aka dauke su.

KU KARANTA: Barawon da yaje sata ya manta da abinda zai sata bayan mata da miji sun dauke mishi hankali a lokacin da suke jima'i

Duk da dai cewa babu wani karin bayani da aka samu dangane da abinda ya sanya ta bar gida da kuma inda take a yanzu, Johnson dai ya bayyana cewa shi bai taba yin lalata da ita ba.

Yarinyar ta bayyana cewa Johnson ne ya dauke ta ya kai ta asibiti domin a zubar mata da ciki. Jaridar Sun-Sentinel ta bayyana cewa an bawa jami'an 'yan sanda damar bincika gidan Johnson, inda kuma suka samu nasarar gano wasu takardu da suke da alaka da zubar da cikin nata.

Yarinyar ta bayyana cewa Johnson ne yayi mata ciki kuma ya dauke ta ya kaita asibiti domin a zubar da cikin.

Yanzu haka dai Johnson yana hannun jami'an hukumar 'yan sanda kuma har yanzu babu lauyan da ya nemi ya tsaya masa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel