Gwamnoni sun cimma sabuwar matsaya a kan biyan sabon karin albashi

Gwamnoni sun cimma sabuwar matsaya a kan biyan sabon karin albashi

- Ma'aikatan gwamnati a wasu jihohin ba zasu samu damar karbar N30,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ba

- Gwamnatin tarayya ta amince da yin karin albashi amma har yanzu bata fara biyan ma'aikata sabon karin albashin ba

- A ranar Litinin kungiyar gwamonin jihohin Najeriya (NGF) ta bayyana cewa kowacce jiha zata yi karin albashi daidai abinda zata iya.

Batun karin sabon albshi da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rattaba wa hannu ya gamu da cikas a wasu jihohin Najeriya, kamar yadda gwamonin suka bayyana.

Legit.ng ta rawaito cewa kungiyar gwamnonin jihohin Najeriya (NGF) ta ce jihohi zasu biya karin albashi ne daidai da zurfin aljihunsu da kuma karfin tattalin arzikin da suke da shi, a saboda haka sun nuna cewa ba kowacce jiha ce zata iya biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi ba.

Shugaban kungiyar gwamnoni kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, shine wanda ya bayyana hakan yayin da yake magana da manema labarai jim kadan bayan kammala taron da suka yi a Abuja.

DUBA WANNAN: An gano abinda yasa Buhari zai wuce kasar Ingila daga Saudiyya

Da yake karantar takardar matsayar da suka cimma yayin ganawarsu, Fayemi ya ce gwamonin sun dauki sabon matakin ne yayin ganawar da suka yi domin tattauna wa a kan nasarar daa aka samu a jihohi wajen kaddamar da biyan sabon karin albashin tun bayan da ya zama doka.

Ya ce duk da gwamnoni sun amince da biyan N30,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi, ya kara da cewa ba majalisar zartar wa ta tarayya (FEC) ce zata yanke shawara a kan abinda zai faru a jihohi ba. Ya bayyana cewa kowacce jiha tana da majalisar zartarwa, wacce alhakinta ne ta yanke shawara a kan yadda jiha zata gudanar da al'amuranta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel