Yanzu Yanzu: Gwamnoni na ganawa a Abuja

Yanzu Yanzu: Gwamnoni na ganawa a Abuja

Gwamnoni a karkashin inuwar kungiyar gwamnonin Najeriya na cikin ganawa a Abuja a yanzu haka domin daidaita matsayinsu akan wasu muhimman lamuran da suka shafi kasar.

Taron wanda ke gudana a yanzu haka a Transcorp Hilton hotel, ya samu hallaran mafi akasain gwamnoni, ciki harda Dapo Abiodun na jihar Ogun, wanda ya shigo yan lokuta kadan da suka gabata.

A ajandar taron harda “Karin bayani akan ganawar gidauniyar Bill and Melinda Gates a Seattle, a ranakun 12-13 Nuwamba da sauran su.

“Karin bayani akan ragin tallafi na kasafin kudi.

"Shawara akan kudaden da aka kwato ta sanadiya gwamnatocin jiha.

"Jawabi daga kwamitin wucin gadi na tattalin arziki akan danyen mai da sauan muhimman asusun tarayya karkashin jagorancin Gwamna Nasi El-Rufai.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da sufeton dan sanda da wani mutum guda a garin Abuja

"Karin bayani akan lamarin cibiyar lafiya na Primary Health Care Under One Roof (PHCOUR) da sauran lamuran da suka shafi lafiya."

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa watan Satumban 2019 ne gwamnatin tarayyar Najeriya za ta soma zare kudinta da ta ba wasu gwamnonin jihohi bashi a shekarar 2016 bayan sun gaza biyan albashin ma’aikata.

Hukumar dillacin labarai na kasa, NAN ta rahoto cewa gwamnatin Buhari za ta cire Naira biliyan 614 daga asusun wadannan gwamnoni sa su ka karbi aron kudi a hannun gwamnatin tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel