Sabon watan Musulunci: Sarkin Musulmi ya yi kira ga Musulmai su nemi watan Rabiul Awwal

Sabon watan Musulunci: Sarkin Musulmi ya yi kira ga Musulmai su nemi watan Rabiul Awwal

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi kira ga al’ummar Musulman Najeriya dasu fita neman sabon jinjirin watan musulunci na Rabi’ul Awwal.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito Sultan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta samu sa hannun shugaban kwamitin addinin musulunci ta fadar Sarkin Musulumi, Farfesa Sambo Junaidu.

KU KARANTA: Mamakon ruwan sama ya yi ajalin wata budurwa a cikin keke Napep a Kaduna

Idan za’a tuna, a lissafin kwanakin shekarar Musulunci na 1441, yau Litinin, 28 ga watan Oktoba shi ne ya yi daidai da 29 ga watan Safar, da wannan ake sa ran shiga watan Rabiul Awwal.

A cikin wannan wata na Rabiul Awwal ne musulmai suke gudanar da bikin Maulidi inda suke murnar zagayowar ranar haihuwa Annabin tsira Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.

Sanarwar ta ce: “Ana sanar da al’ummar Musulmai cewa yau Litinin 28 ga watan Oktoba ya yi daidai da 29 ga watan Safar na shekarar 1441 bayan Hijira shi ne ranar da za’a nemi sabon waran Rabiul Awwal.

“Da wannan ake kira ga Musulmai game da neman jinjirin watan Rabiul Awwal, ana kira ga jama’a dasu fita bayan faduwar rana domin neman watan, kuma su sanar da hakimai da dakatai da zasu sanar da Sultan” Inji kwamitin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel