Yadda zaben kananan hukumomi ke gudana a jihar Kebbi

Yadda zaben kananan hukumomi ke gudana a jihar Kebbi

An fara kada kuri'u lami lafiya a rumfar zabe ta Dakta Gukama mai lamba 007 da kuma rumfar zabe ta G/Kundi a mazabar Nasarawa da ke karamar hukumar Birnin Kebbi amma mutane kalilan ne suka fito zaben.

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN), an fara zaben karamar hukumar ta Birnin Kebbi tun karfe 7 na safiya bayan da aka kawo kayayyakin zaben kuma jami'an zaben suka hallara.

Jami'an Hukumar Zabe na Jihar Kebbi (KEBSIEC) sun isa rumfunan zabe misalin karfe 7 na safe yayin da aka fara jefa kuri'ar farko misalin karfe 8.43 na safe.

Daily Trust ta ruwaito cewa an fara zabe a mafi yawancin rumfunan zabe misalin karfe 9 na safe inda jami'an 'yan sanda suka hallara don tabbatar da tsaro.

DUBA WANNAN: Gidan Malam Owotutu: Gardawa 5 suka yi min fyade, na zubar da ciki har sau 3 - Budurwa

A mafi yawancin rumfunan zaben ana gudanar da zaben da tantance masu zabe a lokaci guda ne sai dai mutanen da suka fito ba su da yawa.

An baza jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya da na Hukumar tsaro ta NSCDC a rumfunan zaben duk da cewa al'umma ba su fito ba sosai.

Jami'in zabe na rumfar zabe ta G/Kundin Zouro, Abidina Abubakar ya ce ya isa rumfar zaben karfe 7 na safe kuma suna tsamanin mutane za su fito domin su kada kuri'unsu.

Wani jami'in zaben a rumfar zaben Dakta Guluma, Faruku Muhammad ya ce dukkan kayayyakin zaben sun iso kuma zaben na tafiya lami lafiya.

Wani mai zabe, Abdulkarim Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana farin cikinsa kan yadda zaben ke tafiya lafiya kuma ya yi addu'an Allah yasa a gama lafiya.

Shima gwamnan jihar, Atiku Bagudu ya ya yi murnar ganin yadda mata suka fito kwansu da kwarkwata.

Yayin kada kuri'arsa a rumfar zaben Mai Alelu a mazabar Nasarawa a Birnin Kebbi, gwamnan ya yabawa KESIEC kan kokarin da tayi na samar da isasun kayayyakin zabe.

Ana gudanar da zabukan ne a kananan hukumomi 21 na jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel