'Ba dukansa aka yi ya mutu ba' - NYSC ta yi karin haske kan mutuwar karamin yaro a Kano

'Ba dukansa aka yi ya mutu ba' - NYSC ta yi karin haske kan mutuwar karamin yaro a Kano

Shugaban Hukumar Kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC) reshen jihar Kano, Ladan Baba ya musanta rahotannin da ake yada na cewa wani dan yi wa kasa hidima a karamar hukumar Bebeji ya yi wa yaro duka har sai da ya mutu.

An ce marigayin ya fusata dan yi wa kasa hidiman ne yayin da ya hangi yaron yana kwashe 'ya'yan itatuwa da aka tattara domin rabawa sauran yara baki daya.

Rahotannin sun ce dan yi wa kasa hidimar ne ya sumar da yaron.

Sai dai sanarwar da Baba ya fitar a ranar Juma'a ta saba da rahoton da aka bayar a baya, ya ce dan yi wa kasa hidimar ya bi yaron da gudu ne shi kuma yaron ya fadi ya buga kansa da bangon kofar shiga gidan masu yi wa kasa hidimar.

DUBA WANNAN: Gidan Malam Owotutu: Gardawa 5 suka yi min fyade, na zubar da ciki har sau 3 - Budurwa

Ya ce an garzaya da yaron zuwa asibiti nan take amma likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu.

Sanarwar ta ce, "An janyo hankalin hukumar NYSC na jihar Kano kan wannan batun.

"Muna juyayin rasuwar yaro dan shekaru 8, Hassan Suleiman dan aji 3 dalibin makarantar Islamiyya ta tsohuwar masallaci. Muna son mu bayyana cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 3.17 na rana a ranar Alhamis, 25 ga watan Oktoba a garin Bebeji a karamar hukumar Bebeji na jihar Kano inda wani dan yi wa kasa hidima, Jepthan Peter Makwin ya bi wani yaro da ya shigo gidansu don tsinkar 'ya'yan itatuwa daga bishiya.

"A garin gudu ne yaron ya fadi ya buga kansa da bangon kofar gidan. An garyaza da shi asibiti nan take amma daga bisani likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu."

A cewarsa, wani da abin ya faru a gabansa ya ce akwai alaka mai kyau tsakanin 'yan yi wa kasa hidimar da al'ummar unguwar kuma yara sun saba zuwa gidan.

Baba ya ce dan yi wa kasa hidimar yana hannun 'yan sanda inda ake gudanar da bincike kuma ya ce ya jagoranci tawaga daga hukumar ta NYSC inda suka kai ziyarar ta'aziyya zuwa gidan iyayen yaron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel