Tafawa Balewa ya san akwai man fetur a Arewa amma bai hako ba - Tsohon Ambasada

Tafawa Balewa ya san akwai man fetur a Arewa amma bai hako ba - Tsohon Ambasada

Tsohon Ministan Ilimi, Kimiyya da Fasaha, Ambasada Yerima Abdullahi ya ce Farai ministan Najeriya na farko, Abubakar Tafawa Balewa (1912-1966) ya san cewa akwai danyen mai a Arewa amma bai hako man ba.

The Punch ta ruwaito Abdullahi ya ce Balewa ya yi hakon man ne tun a zamaninsa don yana son jikokinsa da za su taso a gaba su amfana da man fetur din.

Ya ce gano man fetur a Arewa musamman wanda aka gano a yankin da ake kira Gongola Basin ya kunyata wadanda ke kiran arewa 'kaska' a Najeriya.

Hukumar Man Fetur ta Najeriya (NNPC) a baya-bayan nan ta sanar da gano sinadarin hydrocarbon a Kolmani River II Well da ke Benue da Gongola Basin a Arewa maso Gashin kasar.

DUBA WANNAN: Gidan Malam Owotutu: Gardawa 5 suka yi min fyade, na zubar da ciki har sau 3 - Budurwa

Bayan wannan nasarar gano man fetur da aka yi, wadanda ke yi wa Arewa gori za su hadiye maganganun da suke yi a baya.

Ya ce, "Nesa ta matso kusa. Munyi sa'a cewa man fetur din da aka gano a Bauchi ne wato jihar mu. Muna fatan za a gano wasu ma'adinai kamar gwal, copper da sauransu a arewa ba man fetur kawai ba.

"Akwai man fetur da iskar gas tun kafin a haife mu. Magabatan mu ciki har da gwamnatin Tafawa Balewa sun sani amma ba su yi hayaniya kan batun ba sai suka bar wa na baya su zo su amfana da shi."

Abdullahi bai bayyana ko gano man fetur din zai sanya yankin ta fara neman 'yan cin ta ba kamar yadda sauran yankuna masu man fetur keyi amma ya ce dama Arewa ba ta taba hana wata yanki iko da ma'adanan ta ba.

Ya kara da cewa, "Muna murna cewa an gano man fetur a arewa kuma zai karawa Najeriya arziki don mun yarda da hadin kan kasar nan. Bama bakin ciki don wata yanki tana amfana da albarkar da Allah ya yi mana."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel