Kullu Nafsin Za'ikatul Maut: Maciji ya hallaka wani dalibi a jami'ar jihar Bauchi

Kullu Nafsin Za'ikatul Maut: Maciji ya hallaka wani dalibi a jami'ar jihar Bauchi

A ranar Larabar makon da ya gabata ne 23 ga watan Oktobar nan Allah ya yiwa wani dalibi rasuwa a jami'ar jihar Bauchi dake Gadau wato (Bauchi State University, Gadau)

Dalibin wanda aka bayyana sunan shi da Shamsu Yahaya Gakaka, dan asalin karamar hukumar Alkaleri ne dake jihar Bauchi.

Dalibin ya rasu sakamakon wani maciji da ya sare shi a cikin makarantar. Sun yi kicibus da macijin ne a lokacin da ya fito diban ruwa a burtsatse bayan an kammala sallar Isha'i.

Shamsu dai na cikin tafiya sai tsautsayi ya sanya shi ya taka macijin, cikin gaggawa macijin ya sare shi a kafa bayan yaji zafin takun da yayi masa, a lokacin aka garzaya da shi zuwa asibiti, amma an ce idan lokaci yayi koda babu ciwo aje, ballantana kuma wannan da ciwon.

KU KARANTA: Masu cewa mun ki yin aure idan da gaske suke su fito su aure mu - Fati Baffa Fagge

Shamsu dalibi ne a bangaren lafiya, kuma yana aji na uku wato (300 Level).

Kafin wannan lamarin ya faru Shamsu ne shugaban dalibai 'yan asalin karamar hukumar Kirfi da Alkaleri dake jihar Bauchi.

Haka zalika a yayin da wani ke murna da samun cigaba a rayuwa wasu kuma a lokacin ne suke kuka, a cikin makon nan ne wani mutumi dan shekara 40 ya riga mu gidan gaskiya sanadiyyar hatsarin mota da ya ritsa da shi.

Mutumin dai an bayyana cewa ya shafe shekaru da dama yana neman aiki bai samu ba sai wannan karon ya samu, Allah yayi karshen shan ruwan shi kenan.

Allah dai ya jikansu ya gafarta musu, muma idan ta mu ta zo Allah yasa mu cika da imani. Amin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel