Mahaifiya ta antayawa 'dan ta ruwa zafi yayin da ya ke barci

Mahaifiya ta antayawa 'dan ta ruwa zafi yayin da ya ke barci

Wata jarumar fim, Angela Okorie ta wallafa a shafin ta na Instagram yadda wata mata a ranar Juma'a ta antayawa 'dan dan Destiny dan shekaru 17 ruwan zafi yayin da ya ke barci.

A cewarta, lamarin ya faru ne misalin karfe 5.48 na asubahi inda mahaifiyar ta antayawa dan ta ruwan zafin lokacin yana shararar barci.

Ta yi ikirarin cewa ta aikata hakan ne don yaron bai tashi da wuri ya debo ruwa da wanke wasu kaya ba.

DUBA WANNAN: Na yi wa 'ya'ya na biyu fyade ne don gwada kuzari na - Mahaifi

Jarumar ta kuma bayyana cewa akwai yiwuwar mahaifiyar yaron mai shekaru 29 ta gamu da wasu matsaloli na kwakwalwa tun tana 'yar shekaru 13 a duniya kuma wai kuma maza uku sun mata fyade tun tana karama.

Jarumar ta roki 'yan Najeriya su taimaka su raba yaron da mahaifiyarsa don akwai alamun tana iya yin ajalinsa wata rana.

Ta kuma yi ikirarin cewa mahaifiyar ba ta san mahaifin yaron ba don ta samu cikinsa ne sakamakon fyade da wasu su ka yi mata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel