Manoman tumatur sun nemi wata alfarma daga wurin Shugaba Buhari

Manoman tumatur sun nemi wata alfarma daga wurin Shugaba Buhari

Manoman kayan miya a garin Gashua, Jihar Yobe sun roki Shugaba Muhammadu Buhari ya haramta shigo da tumaturin kasashen waje cikin kasar don taimakawa manoma na gida Najeriya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN ta ruwaito cewa manoman sunyi wannan kirar ne a zantawar da suka yi da manema labarai da lokuta daban-daban.

Wani manomin tumatur, Mallam Musa Maitumatur ya ce shigo ta tumaturin kasashen waje ne ke kawo cikas ga cigaban noman tumatur a gida Najeriya.

Ya ce, "Matsalar manoman kayan miya ta fara ne daga rashin ingantaccen hanyar da za a adana kayan miyan na tsawon lokaci da wurin ajiya kuma babu wanda ke kokarin tallafawa manoma na gida saboda ana shigo da tumatur daga kasashen waje."

DUBA WANNAN: Na yi wa 'ya'ya na biyu fyade ne don gwada kuzari na - Mahaifi

Wani manomin, Ali Katuzu ya ce manoman na asarar a kalla kashi 50 cikin 100 na abinda suka noma saboda rashin ingantaccen wurin ajiya inda ya kara da cewa tilas ke saka manoman su yanka tumaturin su busar saboda rashin hanyar ajiyar.

Ali ya shawarci gwamnati ta kirkiri shiri tsakanin manoma da 'yan kasuwa ta yadda za a samar da kamfanonin sarrafa tumatur a jihar.

Da ya ke tofa albarkacin bakinsa, wani manomi, Habu Sani ya ce suna noman rani kuma suna iya samar da tumaturin da zai wadatar da yankin Arewa maso Gabas amma kallubalen ajiyar, zirga-zirga da sarrafawa ce suke fama da ita.

Ya ce, "Idan ana son kayayyakin cikin gida su inganta, dole sai gwamnati ta haramta shigo da tumaturin kasar waje kamar yadda ta yi a bangaren shinkafa.

"Manoman Najeriya ba za su iya bunkasa ba muddin ba a haramta shigo da tumaturin kamfanoni na kasashen waje ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel