Makahon Farfesa na BUK ya lashe kyautar motar SUV na N8.8m

Makahon Farfesa na BUK ya lashe kyautar motar SUV na N8.8m

Farfesa Jibrin Diso, makahon farfesa a jami’ar Bayero, Kano a ranar Juma’a ya lashe kyautan motar naira miliyan takwas ta hanyar gasa da mutane 699.

Sakataren din-din-din na ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Mista Ernest Umakhihe a lokacin da yake mika motar a Abuja ya ce lashe kyautar da Diso ya yi nufi ne na Allah.

Lokacin da yake bayani kan yanda makahon makahon jami’ar ya lashe kyautar motar ta SUV, Umakhihe ya bayyana cewa ya jagoranci tawagar mutane 700 wadanda suka shiga gasar hadin gwiwa na hukumar tsare-tsare da kungiyar cigaban kasa zuwa wani taro a Asaba, Delta.

Ya bayyana cewa bayan ganawar kwana biyu, sun kuma kai ziyaran gani da ido zuwa kamfanin Innoson Vehicles Motor, IVM, a Nnewi don ganin matakin jajircewar kamfanin kere-keren ta fannin bunkasa tattalin arzikin kasar.

Ya bayyna cewa cikin farin cikin ziyarar ne Shugaban kamfanin ya ba tawagar sabuwar mota kirar IVM Ikenga.

Sakataren yace an samu rudane dangane da yanda za a zabi mamallakin motan cikin tawagar 700.

A cewarsa domin yin adalci sai kungiyar ta yanke shawarar sanya gasar zane inda a ciki ne Diso ya yi nasara.

Mista Umakhile ya taya wanda ya lashe kyautan murna ya kuma mika godiya ga IVM akan goyon bayan shirin bunkasa tattalin arzikin kasar.

Ya jaddada jajircewar gwamnati wajen goyon baya da kuma karfafa kananan kamfanoni ta hanyar aiwatar da manufofin kamfanonin kasar wajen tabbatar da siyan kayan da aka sarrafa a Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu - Yanzu: Buhari ya sauka Najeriya daga kasar Rasha

Yayin da yake mayar da martani, Diso ya mika godiya ga ma’aikar sannan ya bayyana nasarar da ya samu a matsayin nufi na Allah.

Farfesan ya bukaci gwamnati a dukkan matakai dasu samar da wata dama ga nakasassu domin su samu shiga gwamnati da kuma shugabancin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel