Zaben Nasarawa ta Kudu: Al-Makura ya sake yin nasara kan Adokwe a kotun daukaka kara

Zaben Nasarawa ta Kudu: Al-Makura ya sake yin nasara kan Adokwe a kotun daukaka kara

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Makurdi ta bawa Sanata Umaru Tanko Al-Makura nasara.

A yau Juma'a ne kotun ta yanke hukunci kan karar da Sanata Suleiman Adokwe na jam'iyyar People Democratic Party, (PDP) ya shigar na kallubalantar nasarar Al-Makura na jam'iyyar All Progressives Congress, (APC).

Alkalan kotun, Mai shari'a Jummai Hannatu Sankey da Joseph Eyo Ekanem sun yi watsi da karar da aka shigar a gabansu kan kallubalantar zaben.

DUBA WANNAN: Bin diddigi: Shin gaskiya ne CIA ta yi hasashen cewa Najeriya za ta rushe kamar yadda Jega ya fadi?

Daya daga cikin alkalan Sanata Al-Makura, Dr Mubarak Tijani Adekilekun ya ce, "Nayi farin ciki da hukuncin kotun, wannan kotun daukaka karar ta sake tabbatar da nasarar Sanata Al-Makura, wannan nasara ce ga Demokradiyyar Najeriya.

"Yanzu mutane za su ga cigaba kuma za su more romon demokradiyya a jiha da kuma kasa baki daya."

A martaninsa, Sanata Suleiman Adokwe ya shaidawa Daily Trust cewa, "Wannan kadara ce ta Allah, Ina godiya ga Allah da ya bani ikon amincewa da hukuncin kotun cikin kwanciyar hankali."

Idan ba a manta ba Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC ta bayyana Al-Makura a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar Dan Majalisar Tarayya na Fabrairun 2019 bayan ya samu kuri'u 113,156 inda ya doke mai biye masa na jam'iyyar PDP, Adokwe da ya samu kuri'u 104,595.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel