Ganduje ya raba kayan makaranta da littafan karatu kyauta ga daliban firamare a Kano

Ganduje ya raba kayan makaranta da littafan karatu kyauta ga daliban firamare a Kano

Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje a ranar Alhamis 24 ga watan Oktoba ya kaddamar da soma bayar da littafan karatu da kayan makaranta ga daliban firamare a Kano.

Wannan tsarin zai samar da kayan makaranta guda 779,522 zuwa ga daliban makarantun firamare dake a kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

KU KARANTA:Iya kudinka iya shagalinka: Abubuwan nishadi 10 da zaka iya yi da N5000 a Legas

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito mana cewa, rabon wadannan kaya na daga cikin tsarin Gwamna Ganduje na bayar da ilimi kyauta daga firamare har zuwa sakandare.

A wurin taron kaddamar da rabon kayan wanda aka yi a makarantar firamare ta Mariri Special Primary School dake karamar hukumar Kumbotso, Ganduje ya ce wannan kadan kenan daga cikin kokarin gwamnatinsa na ganin ko wane yaro jihar ya samu ilimi kyauta.

A cewarsa, a Kumbotso kawai an raba kayan makarantar guda 29,480 inda aka bai wa daliban aji daya na makarantu 78 dake karamar hukumar.

Bugu da kari, an raba littafan karatu guda 500 na turanci da na Hausa 500 a wurin taron. Ganduje ya kara da cewa gwamnatinsa ta soma kimanin naira miliyan 200 ga ko wace makaranta a ko wane wata.

Makarantun firamaren guda 1180 inda yawan dalibansu ya kama 834,366 kuma kudin da za a rinka basu a wata-wata zai kama jimillar N2.4bn kenan a shekara.

Haka zalika, gwamnan ya ce, gwamnati ta kashe kimanin naira miliyan 381 wurin dinkawa sabbin dalibai kayan makaranta.

https://dailynigerian.com/ganduje-distributes-free-uniforms-instructional-materials-to-kano-pupils/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel