Iya kudinka iya shagalinka: Abubuwan nishadi 10 da zaka iya yi da N5000 a Legas

Iya kudinka iya shagalinka: Abubuwan nishadi 10 da zaka iya yi da N5000 a Legas

Birnin Legas gari ne mai matukar kayatarwa da abubuwa ban sha’a masu tarin yawa. Wani abin mamaki game da garin shi ne bai fiye tsadar rayuwa ba kamar yadda mutane ke dauka.

Ga jerin abubuwa 10 na nishadi da naira 5000 ko ma kasa da haka za su biyawa mutum bukata a Legas:

1. Kasuwar sarrafa ababen kwaliya ta Lekki

Wannan kasuwar ta Lekki wuri ne inda ake sarrafa kayayyakin kawata daki wadda aka fi sani da Kasuwar Jakande. Kasuwace inda zaka iya samun kayan kawata dakinka daga naira 500.

KU KARANTA:Rashin tsaro: IG zai shiryawa jami’an ‘yan sanda taro na musamman na kwana 3

2. Ziyarta Freedom Park

Freedom Park wani wurin shakatawa ne inda mutum kan iya zuwa domin samun nishadi. Duk wani abinda zaka yi a wannan wurin kyauta ne amma kudin shiga ne naira 200 kacal.

3. Rangadi a Moist Beach

Moist beach club na nan ne a Oniru, unguwar da tayi fice a jihar Legas. Da naira 1000 kacal zaka iya shiga wanna wuri domin shakatawa da samun nishadi, haka yake yanda kasan ka je Miami ta Amurka.

4. Ziyartar cibiyar al’adu ta kasa wato National Arts Theatre

National Arts Theatre na nan ne a shiyar Iganmu. Wuri ne inda akasarin ‘yan masana’antar wasan kwaikwayo ke zuwa. Zaka iya zuwa wurin domin hutawa musamman a karshen mako.

5. Zuwa silma domin kallo fim

Akwai gidajen silma inda ake haska fim a Legas. Daga naira 1000 zuwa 3000 shi ne kudin da ake biya domin kallon fim a silma.

6. Shagon littafai na Jazzhole

Masu sha’awar karance-karance za su iya zuwa wannan wuri domin kashe akalla naira 2000 na siyan littafi tare da dan abin sawa a baka.

7. Wurin wasanni na Rufus and Bee

Da naira 5000 kacal zaka buga wasanni da dama a Rufus and Bee. Har ila yau kuma akwai wurin cin abinci a wannan wurin.

8. Hawan doki a Oniru Private Beach

Da naira 100 kacal zaka hau doki a wannan wurin. Akwai mawakan Najeriya da dama da suka sha yin bidiyo a wurin.

9. Ziyartar Gidan tarihi na kasa

Idan baka zuwa gidan tarihi ba zaka san tarihin Najeriya ba. zuwa wannan zai sa ka kara sanin Najeriya sosai.

10. Ziyartar Lambun Lekki

Akwai shuke-shuke da yawa a wannan wuri. Haka kuma an keba kadan daga cikin wadansu namun daji. 100 ne kudin shiga na yara manya kuma naira 500 kacal.

https://thenationonlineng.net/10-fun-things-to-do-in-lagos-with-n5000-or-less/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel