Hotuna: Matashin saurayi mai basira ya kera sabuwar mota a Najeriya

Hotuna: Matashin saurayi mai basira ya kera sabuwar mota a Najeriya

- Wani matashin saurayi mai basira ya kirkiri sabuwar mota da hannun shi

- Matashin ya kera motar ne ta hanyar amfani da karafuna da injin mashin

- Haka kuma matashin ya samo tankin injin janareto tare da tayoyin babur wajen hada wannan mota tashi

Wani matashin saurayi dan shekara goma sha tara (19) mai suna Izunwa Justin Chinedu, wanda ya fito daga kauyne Amurie Omanze dake karamar hukumar Isu cikin jihar Imo, ya kera wata sabuwar mota.

Matashin saurayin bayan kammala kera motar tashi ya sanyawa motar suna G-Wagon, matashin yayi amfani da injin mashin da kuma tankin injin janareto wajen tada injin motar.

Bayan haka kuma saurayin yayi amfani da karafa kala-kala inda ya hada gangar jikin motar, sai dai kuma motar ya yi ta tsirara ne ba tare da ya rufe ta ba.

Amma dai rahotanni sun bayyana cewa an gwada amfani da motar ta tashi kuma tayi tafiya kamar yadda ya kamata.

Wannan yasa mutanen kauyen suka cika da farin ciki don ganin dan kauyensu ya samu irin wannan gagarumar nasara ta kera mota da hannun shi.

KU KARANTA: Asiri ya tonu: Yadda aka kama fastoci biyu sunyi amfani da mace daya wajen nuna mu'ujizar karya (Bidiyo)

Akwai mutane masu basira ta kirkire-kirkire a Najeriya wadanda da ace gwamnati za ta mayar da hankali a kansu ba karamin cigaba za su kawowa Najeriya ba.

A kwanakin baya ma an samu wani dalibi a jihar Kano da ya kware wajen kirkire-kirkiren motoci jiragen yaki da dai sauran su.

Sai dai mutane da yawa na ganin cewa matasan na wahalar da kansu ne kawai domin babu wani abu da gwamnati za ta yi domin ganin basirar su ta amfani kasa.

Hotuna: Matashin saurayi mai basira ya kera sabuwar mota a Najeriya
Hotuna: Matashin saurayi mai basira ya kera sabuwar mota a Najeriya
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel