A Zango ya raba guraben tallafin karatu ga fadar Sarkin Zazzau, APC da PDP

A Zango ya raba guraben tallafin karatu ga fadar Sarkin Zazzau, APC da PDP

Wani hanzari ba gudu ba game da tallafin karatun da shahararren dan wasan kwaiwakyon nan, Adamu Zango ya yi ikirarin bayarwa shine yadda babu wanda ya fito a fili ya amsa cewa ya ci gajiyar wannan tallafi daga cikin mutane 101 da jarumin yace ya tallafa ma wa.

Sai dai wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ya nuna cewa har yanzu ba’a tantance daliban da zasu ci gajiyar wannan tallafi ba, don haka ba a riga an zabosu ba, kamar yadda shugaban makarantar, Dakta Shamsuddeen Aliyu ya bayyana.

KU KARANTA: Tsunstun daya kira ruwa: Malamin daya zakke ma yarinya ya gamu da daurin shekaru 60

Majiyar Legit.ng ta ruwaito akwai lauje cikin nadi game da lamarin, saboda tun farko wannan makaranta ba sunan Professor Ango Abdullahi Group of Schools ba, a da can sunanta kenan, amma daga bisani aka canza mata suna zuwa Professors Group of Schools.

Shugaban makarantar, Dakta Aliyu ya bayyana cewa Adam A Zango ya dauki nauyin dalibai 101, amma ba a kai ga zabosu ba, don haka a yanzu babu yaran a kasa, sai dai Zango ya nemi makarantar ta baiwa fadar mai martaba Sarkin Zazzau gurabe 40, sauran kuma a raba ma jam’iyyun APC da PDP.

Sai dai da majiyarmu ta nemi jin ta bakin wani babban bafaden Sarkin Zazzau, Ciroman Shantali, Alhaji Abubakar Ladan game da maganan, sai yace makarantar ta saba baiwa fada guraben tallafin karatu domin a rabar ga talakawa.

“Amma bani da masaniya ko wadannan guraben da suka bamu sun hada har da wanda Adam Zango ya dauki nauyinsu.” Ini shi.

Daga bisani kuma, Alhaji Ladan ya sake kiran wakilin majiyarmu da karin bayani kamar haka: “Shugaban makarantar ya kirani ya fada min cewa zasu bamu guraben karatu guda 40, kuma za’ayi haka ne a wani taro da za’ayi wanda Adam Zango da kansa zai halarta.”

Amma har zuwa lokacin tattara wannan rahoto jam’iyyun APC da PDP basu ce uffan game da wannan batu na guraben karatu ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel