Daukar aiki: Rundunar 'Yan Sanda ta saki sunayen wadanda suka yi nasara

Daukar aiki: Rundunar 'Yan Sanda ta saki sunayen wadanda suka yi nasara

Rundunar 'yan sandan Najeriya (NPF) ta fitar da jerin sunayen wadanda suka yi nasara a jami'an da za su dauka a shekarar 2019 bayan sun shirya musu tambayoyi da gwaje-gwaje a cibiyoyi daban-daban a sassar kasar.

Rundunar 'Yan sandan Najeriyan ne ta sanar da hakan ta shafinta na Twitter @PoliceNG inda ta ce Sufeta Janar na rundunar, IG Adamu Mohammed ya duba kuma ya bayar da umurnin sakin jerin sunayen wadanda su ka yi nasara bayan jarrabawar da aka gudanar.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan kotu ta umurci rundunar 'yan sandan ta dakatar da aikin daukan sabbin ma'aikatan.

Hukumar Kula da Ladabtar da 'Yan sanda (PSC) ce ta shigar da kara a kotu ta bukaci inda ta ke naman Sufeta janar na 'yan sandan, Adamu Mohammed ya dakatar da aikin daukan sabbin 'yan sandan saboda zargin cewa ya yi mata katsalandan cikin aikinta.

DUBA WANNAN: An bankado wani gidan da 'yan mata masu kananan shekaru ke haihuwa don safarar jariran

Daukar aiki: Rundunar 'Yan Sanda ta saki sunayen wadanda suka yi nasara
Daukar aiki: Rundunar 'Yan Sanda ta saki sunayen wadanda suka yi nasara
Asali: Twitter

Amma duk da hakan rundunar ta 'yan sanda ta fitar da sanar da cewa Sufeta Janar din ya bayar da umurnin sakin sunayen.

Sai dai bayan wasu 'yan mintuna bayan fitar da sunayen, rundunar ta 'yan sandan ta cire sanarwar daga shafinta na Twitter.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel