Bin diddigi: Shin gaskiya ne CIA ta yi hasashen cewa Najeriya za ta rushe kamar yadda Jega ya fadi?

Bin diddigi: Shin gaskiya ne CIA ta yi hasashen cewa Najeriya za ta rushe kamar yadda Jega ya fadi?

Tsohon shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Kasa, (INEC), Attahiru Jega ya yi wasu kallamai da suka janyo cece-kuce tsakanin mutane a ranar Laraba yayin jawabin da ya yi wurin taron cika 20 da kafa demokradiyya a Najeriya da mujallar Tell ta shirya a Abuja.

Jega ya yi magana kan karancin 'yarda' a hukumar zaben da hanyoyin da za a magance matsalar.

Amma ya kuma ce Hukumar Leken Asiri ta Amurka, (CIA) ta yi hasashen cewa Najeriya za ta rushe bayan babban zaben 2015.

A cewarsa, idan ba a dauki matakan da suka dace ba wurin yi wa dokokin zabe garambawul, hasashen na CIA zai zama gaskiya.

Jega ya ce, "CIA ta yi tsamanin cewa 2015 'yan Najeriya za su a mutu ko ayi rai ne, kuma Najeriya ba za ta cigaba da kasancewa kamar yadda aka ta ke ba bayan babban zaben 2015 - kuma hakan ta faru kuma idan ba muyi takatsantsan ba, hasashe da aka yi za su zama gaskiya hakan yasa dole muyi da gaske wurin kare darajar dokokin zaben mu kafin 2023."

DUBA WANNAN: An bankado wani gidan da 'yan mata masu kananan shekaru ke haihuwa don safarar jariran

The Cable ta yi bin diddigi kan ikirarin da tsohon shugaban na INEC ya yi kuma ta gano cewa babu wani takamamen takarda da ke nuna cewa CIA tayi wannan hasashen.

Sai dai akwai wani rahoto na Sashin Binciken Sirri na Amurka (NIC) tayi mai taken: "Mapping Sub-Saharan Africa'a Future."

Duk da cewa binciken ya nuna cewa abubuwa za su tabarbare a nahiyar Afirka muddin Najeriya ta rushe, ya ce akwai wasu dalilai na cikin gida da za su tabbatar da hakan ko akasin haka.

Sai dai wannan baya nufin cewa Najeriya za ta rushe. Cibiyoyin Ilimi sun saba irin wannan binciken lokaci zuwa lokaci.

Tunda an tabbatar cewa CIA ba ta yi wannan hasashen ba, babu dalilin da zai sa a rika alakanta shi da babban zaben 2015.

Matsaya

Ikirarin da tsohon shugaban na INEC ya yi na cewa CIA ta yi hasashen Najeriya za ta rushe kuma hakan na da alaka da zaben 2015 ba gaskiya bane don babu wata hujja da ke tabbatar da hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel