Yarjejeniya 9 na cigaba da Buhari yayi da Vladimir Putin na Rasha

Yarjejeniya 9 na cigaba da Buhari yayi da Vladimir Putin na Rasha

Shugaba Muhammadu Buhari da takwararsa na Rasha, Vladimir Putin, sun yi yarjejeniya kan wasu ayyukan amfani ga Najeriya.

Mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan ne bayan ganawar Buhari da Putin a Sochi.

Ga jerin abubuwan alfanun da Buhari da Putin suka yarde:

1. Gyaran matatun man feturin Najeriya tsakanin NNPC da kamfanin man feturin Rasha, Lukoil.

2. Hadakar NNPC da kamfanin Gazprom na Rasha kan farfadowar da arzikin Iskar Gas a Najeriya

3. Kasar Rasha za ta kammala ginin kamfanin kera karafuna da rodi na Ajaokuta

4. Kasar Rasha zata gina layin dogon jirgin kasa na kilomita 1400 daga Legas zuwa Kalaba

5. Kasar Rasha za ta taimakawa Najeriya wajen gina amfanin Nukiliya a Najeriya

6. Rasha za ta sayarwa Najeriya makamai da kuma horar da Sojojin Najeriya

7. Farfado da kamfanin Aluminum Smelter Company of Nigeria, ALSCON, Ikot-Abasi, Akwa-Ibom

8. Rasha za ta taimakawa Najeriya wajen inganta noman alkama

9. Kasar Rasha za ta kara yawan yan Najeriya da take daman zuwa karatu kyauta kasar

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel