Kungiyar Boko Haram ta samu karin mayaka 2000 daga ISIS – Shugaban kasar Rasha

Kungiyar Boko Haram ta samu karin mayaka 2000 daga ISIS – Shugaban kasar Rasha

Shugaban kasar Rasha, Viladmir Putin ya bayyana cewa akalla mayakan kungiyar ta’addanci ta ISI guda 2,000 ne suka shiga cikin kungiyar ta’addanci ta Boko Haram domin kara musu karfi a shekarar 2018.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito shugaba Putin ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a yayin taron kasar Rasha da kasashen nahiyar Afirka dake gudana a birnin Sochi na kasar Rasha.

KU KARANTA: An nada diyar Danjuma Goje mukamin kwamishina a gwamnatin jahar Gombe

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Putin ya bayyana tabbacinsa na ganin Rasha ta taimaka wajen kawar da ta’addanci a Najeriya dama yankin Afirka gaba daya ta hanyar karfafa alakar tsaro da Soji a tsakanin kasashen biyu.

Biyo bayan galaba da kasashen duniya suka samu a kan ISIS a yankin gabas ta tsakiya, yawancinsu sun koma yankin yammacin Afirka domin taimaka ma Boko Haram da ta dade tana addabar Najeriya, Chadi, Nijar da Kamaru.

Wannan ne ya haifar da kafa wata sabuwar kungiyar ta’addanci mai suna Islamic State of Western African Province-ISWAP a shekarar 2015, dalilin kenan daya kara ma Boko Haram kaimi a yan shekarun nan.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada aniyarsa ta sabunta alakar Soji da kasar Rasha, wanda yace ta samo asali kimanin shekaru 59 da suka gabata tun bayan samun yancin Najeriya a shekarar 1960.

“Ta haka ne zamu samu daman sayen makaman Soja cikin sauki da kuma Sojojinmu su samu horo ingantacce tare da sabunta makaman Najeriya zuwa na zamani kamar yadda Putin ya yi alkawari.” Inji Buhari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng