Jerin sunaye: 'Yan sanda na neman wasu 'yan kungiyar asiri hudu ruwa a jallo

Jerin sunaye: 'Yan sanda na neman wasu 'yan kungiyar asiri hudu ruwa a jallo

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Legas ta fara neman wasu 'yan kungiyar asiri hudu ruwa a jallo.

'Yan kungiyar asirin hudu su ne, Mearling, Samuel, Jide da K. infinity. Hakan ya biyo bayan tonon silili da wasu 'yan kungiyar asiri ta Eiye da jami'an 'yan sanda na sashin yaki da masu fashi da makami suka kama a 'yan kwanakin nan suka yi.

Wani Mista Babatunde Shotayo ya shaidawa 'yan sandan cewa 'yan kungiyar asirin ta Eiye suna tilastawa matasa a Legas shiga kungiyar. Wadanda aka gurfanar a kotu bayan kammala binciken sun hada da Temitope Joseph, Adewale Olatokun, Lekan Akinlabi, Alesanmi Sikiru, Olalekan Aina, Fagbayi Lateef da Keji Awunu.

DUBA WANNAN: Da duminsa: FG ta canja wa ma'aikatar sadarwa suna

Bayan samun karar, an bawa shugaban SARS na Iju, ASP Oluwo Wasiu umurnin kamo wadanda ake zargin. Wasiu ya jagoranci tawagarsa zuwa unguwar inda suka kama mutum bakwai da ake zargi. Yayin binciken sun fadi sunayen mutum 4 a matsayin 'yan kungiyar. Daga baya an gurfanar da su a kotu kan laifin shiga kungiyar asiri da tilastawa kananan yara shiga kungiyar.

Kotun ta karanto cewa kai Temitope Joseph, Adewale Olatokun, lekan Akinlabi, Keji Awunu, Fagbayi Lateef da wasu a ranar 10 ga watan Satumban 2019 misalin karfe 9.00 na safe a unguwar Iju da Legas kun hada baki don aikata babban laifi, da haramtaccen taro wanda ya sabawa sashi na 411 na dokar masu laifi na jihar Legas ta 2015.

Dukkan wadanda ake zargin sun musanta laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa kuma kotu ta bayar da belinsu kan N50,000 kowannensu. An ajiye su a gidan yari ta Kirikiri har zuwa lokacin da suka cika ka'idojin belinsu kamar yadda Linda Ikeji Blog ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel