Sarauniyar Ingila ta karrama wata 'yar Najeriya da lambar girmamawa ta OBE (Hotuna)

Sarauniyar Ingila ta karrama wata 'yar Najeriya da lambar girmamawa ta OBE (Hotuna)

Sarauniyar Ingila, Mai Martaba Elizabeth II ta bawa Dakta Nneka Abulokwe daya daga cikin wanda suka kafa Think Tank lambar girmamawa ta Officer of the Order of the British Empire (OBE).

An mika wa Abulpokwe lambar girmamawar ne yayin wani biki da aka shirya a fadar Buckingham cikin bukukuwar ranar zagayowar haihuwar saurauniyar na shekarar 2019.

Yarima William, Duke na Cambridge ne ya mika mata lambar girmamawar a madadin sarauniyar.

Abulokwe ta samu lambar yabon ne ta OBE saboda ayyukan fasahar zamani da inganta kasuwanci da kamfaninta ke yi.

Baya ga kafa Think Tank, Abulokwe kuma ta kafa wani kamfani mai suna MicroMax Consulting.

Sarauniyar Ingila ta karrama wata 'yar Najeriya da lambar yabo na OBE
Dakta Nneka Abulokwe a fadar Buckingham yayin bikin karamawar da Sarauniya Elizabeth II ta shirya
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da duminsa: FG ta canja wa ma'aikatar sadarwa suna

Sarauniyar Ingila ta karrama wata 'yar Najeriya da lambar yabo na OBE
Dakta Nneka Abulokwe a fadar sarauniyar Ingila yayin bikin da aka shirya don karrama ta da lambar girma ta OBE
Asali: Twitter

Fitacciyar mai kamfanin sana'ar kayan gyaran jiki, Tara Fela-Durotoye ta taya Dakta Nneka Abulokwe murna inda ta ce 'muna taya ki murna tare da alfahari da irin ayyukan da ki ke yi' kamar yadda Linda Ikeji Blog ya wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel