Kano ko da me ka zo an fika: An bude gidan sayar da abincin Naira 30 a jihar Kano

Kano ko da me ka zo an fika: An bude gidan sayar da abincin Naira 30 a jihar Kano

- Wani mutmi mai suna Haruna Injiniya ya bude wani gidan sayar da abinci a jihar Kano da mutane za su ci su koshi a naira 30

- Ya ce ya bude wannan gidan sayar da abinci ne saboda maganar da ministan noma Sabo Nanono yayi a kwanakin da suka gabata

- Ya ce yana fata wasu mutanen za su yi koyi da irin wannan abu da yayi domin talakawa su ci abinci su more babu wata damuwa

Tun bayan maganar da ministan harkokin gona Sabo Nanono yayi na cewa mutum zai iya cin abincin naira talatin ya koshi ya sha ruwa a jihar Kano.

Wannan batu na ministan noma ya jawo kace nace matuka a shafukan sadarwa inda mutane ke ganin cewa wannan abu ba zai taba yiwu wa ba.

A yanzu haka dai an bude wani gidan sayar da abinci na naira 30 a unguwar Sani Mai Nagge layin kuka dake cikin karamar hukumar Gwale a jihar Kano.

Mutumin da ya bude gidan sayar da abincin mai suna Haruna Injiniya, ya bayyana cewa ya bude gidan sayar da abincin ne saboda waccan magana da ministan noma yayi, kuma yayi hakan ne domin mutane su ci abincin su koshi ba tare da wta damuwa ba.

KU KARANTA: Dubu ta cika: Katon gardi dake shigar mata yana cutar samari ya shiga hannu

Ya kuma bayyana cewa suna sayar da abincin nasu wanda suka fara wasar-wasar yadda mutum zai ci ya more har ma ya sha ruwa duka kuma a naira talatin.

Haka kuma Haruna Injiniya ya bayyana cewa yana fatan wasu mutanen suma za su yi koyi da shi domin talakawa su amfana ba tare da sun sha wahala ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel