Tsautsayi: Injin nika ya kwashe ma wani yaro y’ay’an maraina a jahar Bauchi

Tsautsayi: Injin nika ya kwashe ma wani yaro y’ay’an maraina a jahar Bauchi

Masu iya magana na cewa tsautsayi baya wuce ranarsa, hakan ne ta kasance a kan wani karamin yaro mai shekaru 14, Bashir Salisu wanda igiyar injin nika ta tsinka masa y’a’yan maraina duka biyu a yayin da yake nika gari.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa Bashir wanda dalibi ne a makarantar sakandari ta Tudun Salmanu dake garin Bauchi ya gamu da wannan ibtila’I ne a yayin da yake nika a kasuwar Muda Lawal.

KU KARANTA: Daga karshe Gwamna Masari ya fidda sunayen sabbin kwamishinoninsa kamar haka

Tsautsayi: Injin nika ya kwashe ma wani yaro y’ay’an maraina a jahar Bauchi
Bashir
Asali: Facebook

Da yake bayyana ma majiyar Legit.ng yadda lamarin ya auku daga gadon asibitin koyarwa na jami’ar ATBU, Bashir yace lamarin ya auku ne a ranar Juma’a da misalin karfe 10 na safe yayin da yake nika da injin, inda ingiyan injin ya kamo wandonsa, nan take ya tsinka masa maraina, sa’annan ya ji masa rauni a mazakuta.

“Na ji zafi sosai, nan da nan aka garzaya dani zuwa asibiti inda aka fara duba ni, amma sai dai likitoci sun tabbatar da cewa maraina na sun tafi kenan har abada, kuma ba za’a iya sanya min wasu ba. Dama ina nika ne domin na koyi sana’ar da zan iya tsayawa da kafata bayan na kammala karatu.”

Shima mahaifin yaron, Malam Salisu Mohammed ya bayyana cewa ya kadu matuka a sakamakon wannan lamari, amma daga bisani ya rungumi lamarin a matsayin jarrabi daga Allah.

“Muna ta cigaba da addu’ar Allah Ya bashi lafiya duk da cewa dai likitoci sun tabbatar mana marainarsa ba zasu sake dawowa ba, babbar matsalarmu a yanzu itace rashin kudin biyan asibitinsa, shi yasa muke amfani da wannan dama domin neman taimako daga gwamnati, kungiyoyi da jama’a.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel